Masu Zanga Zanga Sun Gamu da Cikas a Abuja, Kotu Ta Ba Su Sabon Umarni

Masu Zanga Zanga Sun Gamu da Cikas a Abuja, Kotu Ta Ba Su Sabon Umarni

  • Yayin da ake shirin fita zanga-zanga a Najeriya, Babbar Kotun Tarayya ta dakile amsu shirin gudanar da ita a gobe Alhamis
  • Kotun ta umarci matasan da ke shirin gudanar da zanga-zangar su tsaya iya ka filin wasa na MKO Abiola da ke birnin
  • Wannan mataki na kotun na zuwa ne bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike ya shigar da korafi kan shirin da matasan ke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan masu shirin zanga-zanga a birnin a gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.

Kotun ta umarci masu zanga-zangar ka da su bazama kan tituna inda tta ba su damar amfani da filin wasa na MKO Abiola.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan masu shirin zanga zanga, ta gindaya sharuda masu tsauri

Kotu ta kawo cikas ga masu shirin yin zanga-zanga a Abuja
Masu shirin zanga-zanga sun ci karo da matsala a Abuja bayan hukuncin kotu. Hoto: Nyesom Ezonwe Wike.
Asali: Facebook

Kotu ta yi hukunci kan masu zanga-zanga

Alkalin kotun, Mai Shari'a, Sylvanus Orji shi ya yanke hukuncin a yau Laraba 31 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TheCable ta tattaro cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike shi ya shigar da korafi kan shirin zanga-zangar da matasa ke yi a fadin kasar.

Wannan matakin kotun na zuwa ne yayin matasa suka shirya fita zanga-zanga a gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.

Zanga-zanga: Wadanda ake kara a gaban kotu

Wadanda ake kara a gaban kotu sun hada da Omoyele Sowore da Damilare Adenola da Adama Ukpabi da Tosin Harsogba.

Sauran sune Sifeta-janar na 'yan sanda da kwamishinan 'yan sanda a Abuja da babban daraktan hukumar DSS.

Sai kuma kwamandan hukumar NSCDC da babban hafsan sojojin kasa da na sama da kuma na ruwa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke a Kano ana daf da fita ta gama gari, bayanai sun fito

Kotu ta yi hukunci kan masu zanga-zanga

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun jihar Ogun ta yi hukunci kan korafin da aka shigar kan masu shirin zanga-zanga.

Kotun ta umarci masu zanga-zangar da su gudanar da shirin na su a wurare guda hudu kacal a fadin jihar baki daya.

Wannan na zuwa ne yayin da matasa suka gama shiryawa dmin fita zanga-zanga a gobe Alhamis 1 gaw atan Agustan 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.