NLC
Kungiyoyin sufurin jiragen sama na Najeriya sun shiga yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka fara a fadin kasar nan. Sun umarci mambobinsu su daina aiki.
Gwamnatin tarayya ta gargadi ma'aikata kan shiga yajin aiki da kungiyoyin kwadago suka shirya a fadin kasar nan. Ta ce za su iya fuskantar dauri a gidan kaso.
Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun ce babu ja da baya kan yajin aikin da za su shiga gobe Litinin duk da kokarin majalisar dokokin na hana faruwar hakan.
A wani yunkuri na dakile shirin yajin aikin da aka shirya yi a fadin kasar nan, majalisar tarayya da shugabannin kungiyoyin kwadago sun gana a Abuja.
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kungiyoyin kwagadon NLC da TUC kan tafiya yajin aiki a gobe Litinin. Ministan yada labarai, Idris Muhammad ne ya yi kiran.
Kungiyoyin kwadago sun bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya sanya baki a tattaunawar da ake yi kan mafi karancin albashi domin hana shiga yajin aiki.
A lokacin da dalibai suka fara fargabar makomar jarrabawarsu ta kammala sakandare WAEC saboda yajin aikin kungiyoyin kwadago, hukumar shirya jarrabawar ta magantu.
Kungiyar kwadago ta NLC tafara shirin tsunduma yajin aikin gama-gari saboda gwamnati ta ki amicewa da biyan mafi karancin albashin da zai dace da ma'aikata.
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kungiyoyin kwadago da su hakura da shirinsu na tsunduma yajin aiki saboda kasa cimma matsaya a kan mafi karancin albashi.
NLC
Samu kari