Tinubu Ya Samu Sauƙi a Bukatar da Ƴan Kwadago Suka Gabatar Kan Mafi Ƙarancin Albashi

Tinubu Ya Samu Sauƙi a Bukatar da Ƴan Kwadago Suka Gabatar Kan Mafi Ƙarancin Albashi

  • Ƴan kwadago sun bayyana cewa za su iya rage adadin kuɗin da suke buƙatar a biya a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya
  • Shugaban TUC, Festus Osifo, ya ce gwamnatin tarayya ba da gaske take yi ba da ta gabatar da tayin N60,000 a taron ranar Talata
  • Manyan kungiyoyin kwadago sun jaddada bukatarsu na N494,000 saboda wahalar da ma'aikata ke ciki bayan cire tallafin fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ƙungiyar kwadago ta kasa TUC ta ce da yiwuwar za su sauko daga N494,000 da suke buƙata a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata a Najeriya.

A makon jiya ne dai ƴan kwadagon suka rage yawan kuɗin da suke bukata a matsayin mafi ƙarancin albashi daga N497,000 zuwa N494,000.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan biyan N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya

Bola Tinubu da shugaban TUC.
'Yan kwadago na iya rage bukatarsu a sabon mafi ƙarancin albashi Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Ƴan kwadago za su sassauta bukatar albashi

Da yake jawabi a wani shirin Channels TV na musamnan kan cikar Bola Tinubu shekara ɗaya a mulki, shugaban TUC, Festus Osifo, ya ce ma'aikata na shan wahala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Mun rage adadin daga N497,000 zuwa N494,000, to amma zamu kafe ne a nan? A'a tattaunawa ce, komai zai iya faruwa. Ka da ku manta mun bayar da wa'adi.
"Wannan wa'adin yana nan, idan har gwamnati ta kasa yin abin da ya kamata daga yau zuwa 31 ga watan Mayu ba, zamu iya tsunduma yajin aiki.

A ranar Talata gwamnatin tarayya ta kara N3,000 a N57,000 da ta gabatar a matsayin sabon mafi ƙarin albashi, ya zama N60,000 kenan, rahoton Leadership.

Sai dai ƴan kwadagon sun watsi da sabon tayin gwamnatin, sun dage kan N494,000, inda suka cire N3,000 daga N497,000 da suka nema a baya.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun yi magana kan sake maɗa Sanusi II a matsayin Sarkin Kano

Albashi: Tinubu ba da gaske yake ba

Yayin wannan tataunawa, shugaban TUC ya ce alamu sun nuna gwamnatin tarayya ba ta damu da walwalar ma'aikata ba.

"Dole gwamnati ta kawo ƙarshen wannan tattaunawa kuma ta ɗauki lamarin da muhimmanci saboda tayin N60,000 da ta gabatar a teburin tattaunawa ya nuna ba dagaske take ba.
"Da ba a cire tallafin man fetur ba kuma tattalin arziki bai durkushe haka ba, wannan tattaunawar ba haka za ta kasance ba," in ji shi.

Majalisa za ta binciki babkin CBN

A wani rahoton kun ji cewa Batun korar daraktoci da manyan ma'aikata a babban bankin Najeriya ya ja hankalin majalisar wakilan tarayya ranar Laraba.

Majalisar za ta binciki yadda aka yi aka rubutuwa ma'aikata akalla 600 takardar kora a CBN bayan ta amince da wani kudiri da aka gabatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel