Masu Garkuwa Da Mutane
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa tana matukar jin kunyar yadda ake sace daliban makaranta a kasar nan, cewar Malam Garba Shehu, hadimin shugaban kasa.
Saleh Alhassan, sakataren kasa na kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, yace wasu 'yan bindigan makiyayya ne da suka zama tsageru sakamakon rasa shanunsu da suka.
Dakarun rundunar Operation Thunder Strike da na Div 1 dake Kaduna sun ragargaza maboyar 'yan bindiga dake yankin Buruku a karamar hukumar Chikun ta Kaduna.
Yan bindiga a Abuja sun yi garkuwa da wani ma’aikacin Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya (FCTA) da wasu mutum uku, sun nemi a biya kudin fansa N200m.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Edo ta kama wani mai POS wanda ke taimakawa masu satar mutane wajen karbar kudi daga asusun bankunan wadanda lamarin ya cika da su.
Mai martaba Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, ya ba da labarin yadda ya tsere wa wani yunkurin kashe shi da wasu ‘yan fashi suka so yi.
Rundunar ‘yan sanda ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi masu satar mutane, Abdullahi Danshoho da Illiyasu Salleh, wadanda suka sace marasa lafiya 2 da nas.
Wasu mahara da ake zaton yan bindiga sun kai farmaki wata kasuwa da ke garin Yar' Tasha a cikin unguwar Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Isyaka Amao, shugaban dakarun sojin saman Najeriya yace rundunar sojin Najeriya ta shirya kakkabo 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane dake fadin kasar nan.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari