‘Yan sanda sun ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su, sun kwato makami a Kaduna

‘Yan sanda sun ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su, sun kwato makami a Kaduna

- Yan sanda a jihar Kaduna kubutar da mutane takwas da aka yi garkuwa da su a Galidamawa, Kidandan, da ke karamar hukumar Giwa ta jihar

- Sun kuma yi nasarar kwato wata bindiga kirar AK47

- Kakakin yan sandan jihar, ASP Muhammed Jalige ya tabbatar da hakan, ya ce suna kokarin kamo masu laifin tare da gurfanar da su

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a ranar Talata ta kubutar da mutane takwas da aka yi garkuwa da su tare da kwato bindiga kirar AK-49 a Galidamawa, Kidandan, da ke karamar hukumar Giwa ta jihar.

Kakakin yan sandan jihar, ASP Muhammed Jalige, ya ce dakarun rundunar Operation Puff Adder II da ke aikin sunturi a hanyar yankin Galidamawa/Kidandan ne suka yi kicibis da yan bindigar da tare da mutanen da suka sace.

Jalige ya ce yan ta’addan sun ci na kare a yayinda suka hango jami’an tsaron inda suka yi watsi da mutanen da suka yi garuwa da su da kuma bindigar.

‘Yan sanda sun ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su, sun kwato makami a Kaduna
‘Yan sanda sun ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su, sun kwato makami a Kaduna Hoto: Samuel Aruwan
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: 2023: Takarar Tinubu ta samu gagarumin goyon baya daga gwamnonin arewa da masu ruwa da tsaki

Har ila yau ya bayyana sunayen wadanda aka ceton a matsayin Bala Ibrahim, Ede Gloria daga jihar Ebonyi, Japheth Sani dan jihar Kebbi, Kinsley Edgbue jihar Delta.

Sai Anthony Okafor jihar Anambra, Gabriel Agu jihar Anambra, Chibuzo Nwokorie jihar Anambra, da kuma Ifenyi Samuel jihar Enugu.

Ya ce:

“A ranar 29 ga Maris, da misalin karfe 0600 na dare ne rundunar Operation Puff Adder II da ke aiki a Kaduna yayin da suke sintiri a kan hanyar Galidamawa / Kidandan da ke karamar hukumar Giwa, sun tare wasu gungun 'yan fashi da makami tare da wasu da suka yi garkuwa da su.

"Lokacin da suka hango jami'an sai suka tsere inda suka bar wadanda abin ya rutsa da su da bindiga daya na AK-49 kuma a cikin hakan an samu nasarar ceto mutum takwas ba tare da rauni."

Ya bayyana cewa daga baya wadanda lamarin ya rutsa da su sun bayyana cewa an sace su ne a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kaduna a cikin babbar motar bas a hanyarsu ta zuwa Delta a ranar 29 ga Fabrairu.

Ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a shirye-shiryen haduwa da danginsu.

Kakakin ya ce rundunar ta shirya farauta don cafkewa tare da gurfanar da barayin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi yunkurin juyin mulki a Nijar, amma ba a yi nasara ba

Jalige ya kara da cewa, "Kwamishinan 'yan sanda a Kaduna, Umar Muri, ya yaba da goyon bayan da Sufeto-Janar na' yan sanda ya bayar wajen tura jami’ai da kayan aiki don yaba wa kokarin da rundunar ke yi na magance ayyukan ta'addanci."

A baya mun ji cewa, 'Yan bindiga a jihar Kaduna sun kashe manoma ta guda tara a hare-hare mabanbanta da suka kai a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa a jihar.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, a ranar Alhamis, ya ce yan bindigan sun tare hanyar Dogon Dawa-Kuyello, bayan kauyen Ungwan Jere da ke karamar hukumar Birnin Gwari suka bindige mutum shida.

Mutanen da suka kashe sune: Nura Rufai, Sanusi Gajere, Yakubu Labbo, Usman Dangiwa, Alhaji Abdulhamid da Junaidu Tsalhatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng