Tashin hankali a Kaduna yayin da wasu 'yan fashi suka sace mambobin RCCG 8

Tashin hankali a Kaduna yayin da wasu 'yan fashi suka sace mambobin RCCG 8

- Hare-haren ‘yan bindiga sun sake faruwa a Kaduna a ranar Juma’a, 26 ga Maris

- An yi garkuwa da wasu mambobin Cocin Redeemed of God a kan hanyarsu ta zuwa wani taro

- Har yanzu dalibai 39 da aka fara sacewa a jihar ba su samu yanci ba

Akalla mambobin Cocin Redeemed Christian Church of God takwas yan bindiga suka sace a Kaduna, a ranar Juma’a, 26 ga watan Maris.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa wadanda lamarin ya rutsa da su suna cikin motar cocin ne suna tafiya domin halartan wani taro lokacin da aka kai musu harin.

Legit.ng ta tattaro cewa wani mai amfani da Facebook, Eje Kenny Faraday, ya sanar da labarin a shafinsa tare da hoton farar motar a yammacin ranar Juma'a, 26 ga Maris.

Tashin hankali a Kaduna yayin da wasu 'yan fashi suka sace mambobin RCCG 8
Tashin hankali a Kaduna yayin da wasu 'yan fashi suka sace mambobin RCCG 8 Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: An yankewa wani mutum hukuncin shekara guda a gidan yari kan sata a coci

Ya rubuta cewa:

"Dukkan fasinjojin da ke cikin wannan motar an yi garkuwa da su ne a kan titin Kachia, kilomita 63 daga Kaduna."

Jaridar ta kuma lura da cewa wata majiya ingantacciya da kuma wani jami'in cocin, wanda suka yi magana bisa sharadi sakaya sunansu, sun tabbatar da rahoton.

An ruwaito majiyar ta ce: “Su takwas ne a cikin bas din. Za su je Kachia a shirye-shiryen cocin na bikin Ista. 'Yan bindigar sun fitar da su daga motar bas din sannan suka sanya su a cikin motarsu na aiki. Har yanzu ba su tuntubi cocin ba. ”

A cewar rahoton, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya ce yana ci gaba da bincike kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban Tijjaniya na duniya, Khalifa Sheikh Muhammadu Mahy Nyass

An gano cewa shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na RCCG, Fasto Olaitan Olubiyi, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba, wanda yayi kururuwa sau da dama.

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Katsina sun cafke wasu mutane uku 'yan damfara waɗan da ke damfarar mutane da sunan cewa su aljanu ne.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Gambo Isa, ya bayyana sunayen mutanen; Usman Adamu, 40, Abba Ibrahim, 38, da kuma Abdurrauf Iliyasu, 39.

SP Gambo yace an sami nasarar kama waɗan da ake zargin ne bayan sun kira wata mata mai suna Jamila Sulaiman a waya sun umarce ta da taje kan hanyar fita garin Yar Gamji ta aje kuɗi N150,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel