'Yan bindiga dauke da AK47 sun budewa jigon APC wuta a jihar Delta

'Yan bindiga dauke da AK47 sun budewa jigon APC wuta a jihar Delta

- Wani dan jam'iyyar APC ya bayyana yadda wasu 'yan bindiga suka yi yunkurin kashe shi a jihar Delta

- Har yanzu ba a gano wadanda suke da hannu a tura 'yan bindigan domin su yi ajalinsa ba

- Nan da nan 'yan Najeriya suka fara bayyana damuwarsu akan rashin tsaro da ya addabi kowa

An samu labarin yadda wasu 'yan bindiga suka budewa wani shugaba na jam'iyyar APC wuta, Olorogun Ovoke Shasha a garin Ughelli dake jihar Delta.

Vanguard ta bayyana yadda dan siyasar yake tsaka da tukin motarsa kirar Highlander SUV kwatsam dai yaji ruwan alburusai a ranar Lahadi, 3 ga watan Afirilu.

Majiyoyi sun tabbatar da yadda harbin ya ji masa raunuka a kirjinsa kuma aka yi gaggawar zarcewa dashi asibiti domin kulawa da lafiyarsa.

KU KARANTA: Ana cigaba da neman matukan jirgin saman sojin Najeriya da yayi hatsari a Sambisa

'Yan bindiga dauke da AK47 sun budewa jigon APC wuta a jihar Delta
'Yan bindiga dauke da AK47 sun budewa jigon APC wuta a jihar Delta. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, an yi yunkurun kashe shi ne yayin da yake kan hanyar daukar wasu katukan gayyata a wani shago.

A cewarsa, "Sai da naji a jikina cewa muna cikin matsala sai nasa a juya da motata. 'Yan bindigan suna rike ne da bindigogi kirar AK-p47.

"Daga nan ne suka harbeni a kirji duk da sun so kasheni ne amma basu samu nasara ba. Sun sace min wayata, abin hannuna da sarkata suka tsere."

Rundunar 'yan sandan jihar Delta a halin yanzu sun ce sun fara bincike akan aukuwar lamarin.

KU KARANTA: Hotunan Obasanjo ya cakare tare da gwangwajewa tamkar matashin saurayi

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya zata tilasta dokar dakatar da albashi matsawar ma'aikaci bai yi aikinsa ba ga kungiyar likitoci masu neman kwarewa na Najeriya basu koma kan ayyukansu ba.

Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ne ya sanar da wannan jan kunnen a ranar Juma'a a wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels.

"A ranar Talata, zan gayyacesu don su koma kan ayyukansu. Zan sanar dasu cewa matsawar ba su yi aiki ba gwamnati ba za ta biyasu ba," cewar Ngige.

"Wadanda aka dauka aiki ya kamata su dage wurin kulawa da lafiyar marasa lafiya. Za mu iya neman likitocin gargajiya, bana fatan mu kai nan wurin amma in dai aka kai toh za mu yi amfani da tsumagiyarmu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel