Mun zabi yin garkuwa da mutane ne saboda shine hanya mafi sauki na samun kudi, yan bindiga

Mun zabi yin garkuwa da mutane ne saboda shine hanya mafi sauki na samun kudi, yan bindiga

- An kama wasu gungun yan fashi a jihar Nasarawa

- An rahoto cewa wadanda ake zargin sun fallasa hakan ne a wani jawabi da suka yi wa ‘yan sanda

- ‘Yan sanda za su gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zaran an kammala bincike

Wasu mutane biyu da ake zargi 'yan fashi ne, Abdullahi Danshoho da Illiyasu Salleh, sun bayyana matsayinsu a sace wasu marasa lafiya biyu da wata ma'aikaciyar jinya a wani asibiti a Jihar Nasarawa.

Wadanda ake zargin tare da mambobin kungiyar su sun kai mamaya asibitin Kunwarke da ke Lafia, Jihar Nasarawa, wani lokaci a watan Nuwamban 2020 sannan kuma suka sace marasa lafiya biyu da wata ma’aikaciyar jinya.

An yi zargin cewa sun karbi kudin fansa naira miliyan 6 kafin su sako mutanen da suka sace.

Mun zabi yin garkuwa da mutane ne saboda shine hanya mafi sauki na samun kudi, yan bindiga
Mun zabi yin garkuwa da mutane ne saboda shine hanya mafi sauki na samun kudi, yan bindiga Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta tsare Shugaban PDP mai shekaru 80 a Oyo kan kisan kai

Jami'an Sufeto Janar-Janar na 'yan sanda masu amsa bayanan sirri karkashin jagorancin DCP Abba Kyari ne suka kama Danshoho da Salleh a kwanan nan.

Danshoho mai shekaru 25 wanda ke da aure da yara hudu, ya bayyana cewa shi direban babbar mota ne amma ya shiga satar mutane saboda baya samun kudi sosai daga aikin.

Ya ce, “Na gama NCE a 2020 amma har yanzu ban karbi sakamako na ba. Na zama direban babbar mota amma abubuwa sun yi wuya. Na hadu da abokina, Illiyasu (Salleh), wani lokaci a cikin Satumba 2020 kuma ya gaya mani hanya mai sauƙi na samun kuɗi. Ya gaya min cewa satar mutane ita ce kawai mafita. Ya ce min in nemi masu kudin da za mu sace.”

Ya ce da shi aka sace mutane biyar - na karshen shine a watan Disamba - ciki har da sace makwabcinsa da ya ki ba shi kudi, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa ya ba da bayanan mutumin ga Illiyasu wanda ya shirya sace shi, ya kara da cewa ya samu N100,000 kaso daga kudin fansar da aka biya.

Danshoho ya bayyana cewa, “Illiyasu ne ya shirya aikin na biyu da aka yi cikin nasara. Wannan asibitin shine inda muke yawan zuwa yin magani. Aikina shine in tabbatar cewa shugaban asibitin yana nan. A ranar da muka kai farmaki, na tabbata cewa yana asibiti. Abin takaici, ya sami damar tserewa. Wannan shine dalilin da yasa suka yanke shawarar sace marasa lafiya.

“Bayan wasu kwanaki, sun ba ni N100,000 a matsayin kasona. Ban yi korafi ba saboda sun fada min cewa marasa lafiyar manoma ne kuma ma’aikaciyar jinyar ta fito ne daga dangin talakawa. Daga baya na fahimci sun tara naira miliyan.

KU KARANTA KUMA: Wajabcin bayyana dukiyoyin ma’aikatan Banki: Sabon Shugaban EFCC ya yi daidai, Barista AlBashir Likko

“Bayan mako guda, na kawo aiki na uku. Abokina ne kuma mun saba zama tare. Na yanke shawarar yin garkuwa da shi ne saboda na tabbata iyayensa za su iya biyan kudin sakin nasa. Sun biya miliyan 1.5 kuma na samu N100,000 a matsayin rabona. Lokacin da ya dawo gida rashin lafiya ne na yi nadamar abinda na aikata. Na yi amfani da wani bangare na kudina wajen biyan basussuka a makarantar domin in samu takardar shedata.”

Salleh, mai shekaru 24, ya ce ya shiga harkar kiwon shanu da noma amma ya daina saboda ba su kawo masa kudin shiga ba. Ya ce ya yanke shawarar shiga satar mutane ne "saboda hanya ce mai sauki ta samun kudi."

“Maganar gaskiya ita ce ba ma samun kudi da yawa daga kiwon shanu kuma mutum na bukatar ya zama da saniya tsawon watanni kafin ta isa amfani. Satar mutane na bayar da kudi cikin sauri,” in ji shi.

Da yake bayanin yadda aka yi satar asibitin, ya ce Danshoho, wanda ma'aikatan jinyan suka yi wa farin sani, ya yi kamar ya zo ne don maganin ciwon kai.

Ya ce, “Ina waje. 'Yan kungiyata, Maigari, Bodejo da sauransu (gaba daya) suka shiga asibitin amma ba su ga darektan ba. Kamar ya ji harbin bindiga ne ya tsere kafin su kai gareshi. Daga nan sai Maigari ya yanke shawarar sace marasa lafiya biyu da kuma wata nas.

“Bayan an biya fansa, sai na samu N200,000 kuma na fusata. Na yi barazanar tona musu asiri idan ba su ba ni karin kaso ba. Na samu karin N100,000 amma ban san ainihin adadin da aka karba ba.”

A wani labarin, an harbe mai taimakawa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Alhaji Abba Abbey Gidan Haki, wanda ’yan bindiga suka sace a daren Alhamis a Sokoto. Anyi jana'izar shi a daren Juma'a, The Nation ta ruwaito.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Sheikh Usman dan Fodiyo dake Sokoto, Sheikh Abubakar Shehu Na Liman ne ya jagoranci sallar jana’izar.

Sallar jana’izar ta samu halartar Sanata Wamakko, Ministan Harkokin ’Yan sanda, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi da shugaban riko na APC na jihar Sokoto, Alhaji Isa Sadiq Achida.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng