Muna matukar jin kunyar yadda ake sace dalibai a kasar nan, Fadar shugaban kasa

Muna matukar jin kunyar yadda ake sace dalibai a kasar nan, Fadar shugaban kasa

- Sace 'yan makaranta da ake yi a Najeriya, lamari ne dake matukar kunyata shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Mallam Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a fannin yada labarai ya sanar da hakan

- Hadimin shugaban kasan yace duk abinda ke faruwa a kasar nan a kowacce rana yana isa wurin Buhari ta kafafen yada labarai

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa tana matukar jin kunyar yadda ake sace daliban makaranta a kasar nan.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a harkar yada labarai, Garba Shehu, ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Yace yadda ake yawan sace 'yan makaranta yana matukar baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kunya a gida Najeriya da ketare.

Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi a shirin gari ya waye na gidan talabijin din Channels.

KU KARANTA: Ta'addanci, sauyin yanayi, rashin tsaro, manyan kalubale ne garemu, Buhari

Muna matukar jin kunyar yadda ake sace dalibai a kasar nan, Fadar shugaban kasa
Muna matukar jin kunyar yadda ake sace dalibai a kasar nan, Fadar shugaban kasa. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamna Abiodun da Bankole sun shiga ganawar sirri

Shehu yayi jawabi a kan koma bayan da aka samu a bangaren garkuwa da 'yan makaranta ballantana a yankin arewa

Ya tabbatar da cewa shugaban kasa ya san komai dake faruwa a kasar nan inda ya kara da cewa "mafi gaggawan hanyar isar da sako ga shugaban kasa shine ta manema labarai da kuma fallasa duk wani mugun abu dake faruwa kasar nan."

Shehu yace Buhari na da ra'ayin hada kan 'yan Najeriya tare da kawo karshen matsalolin tsaron da suka addabi kasar nan.

Ya kara da jaddada cewa 'yan Najeriya suna morar 'yancin fadin ra'ayinsu karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A bangaren ta'addanci, ya jajanta yadda wasu masu yada labarai ke bayyana labaran miyagu tamkar wasu masu aiki nagari.

A wani labari na daban, darakta janar na hukumar Zakkah da Hisbah na jihar Kano, Safiyanu Abubakar, yace ana shirin mayar da biyan Zakka ya zama wajibi ga dukkan 'yan siyasa kafin su tsaya takara a jihar.

Abubakar ya sanar da hakan a ranar Alhamis a ofishinsa yayin rantsar da kwamitin mutum 11 na karbar Zakka a jihar.

Kamar yadda yace, wannan al'amarin ana son tabbatar dashi ne domin taimakon mabukata a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel