Bayan karbar N5m, yan bindigar da suka sace malami da wasu 11 sun saki gawarwaki 4

Bayan karbar N5m, yan bindigar da suka sace malami da wasu 11 sun saki gawarwaki 4

- Har yanzu yan bindiga sun ki sakin malamin nan na Kano Sheikh Abdullahi Shehu Mai Annabi bayan biyan kudin fansa

- Maimakon haka ma, maharan sun saki gawarwakin mutum hudu cikin wadanda aka sace tare da Mai Annabi

- A yanzu suna neman a cika masu naira miliyan 5 kan kudin fansar da aka biya a baya kafin su sake su

Har yanzu malamin nan na Kano, Sheikh Abdullahi Shehu Mai Annabi, wanda yan bindiga suka yi garkuwa da shi tare da wasu mutane 12 a kan hanyarsu ta zuwa jihar Zamfara don halartar Maulud a garin Anka yana tsare, Daily Trust ta ruwaito.

Dan malamin, Isyaku Abdullahi Shehu, ya ce yan bindiga sun sace malamin tare da wasu mambobin tawagarsa 12, ciki har da ’yan’uwansa da dalibai, dukkansu daga yankin Rimin Kebe da ke karamar Hukumar Ungogo a Kano.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya sun yi wa Buhari zanga zanga a hanyar shiga gidansa na Landan

Bayan karbar N5m, yan bindigar da suka sace malami da wasu 11 sun saki gawarwaki 4
Bayan karbar N5m, yan bindigar da suka sace malami da wasu 11 sun saki gawarwaki 4 Hoto: PremiumTimes.ng
Asali: UGC

Kimanin makonni uku da suka gabata ne aka sace su a kusa da garin Sheme da ke jihar Katsina, maharan sun kuma nemi yan uwansu su biya naira miliyan 10.

Ya ce da farko sun bukaci a ba su naira miliyan 15 amma bayan tattaunawa, sai masu garkuwar suka amince su karbi naira miliyan 10.

“Mun riga mun tattara kuma mun gabatar da naira miliyan 5 ga masu satar. Amma da muka isa wurin sai suka umurce mu da mu je mu dauki mutanenmu, sai kawai suka kawo gawarwaki hudu daga cikinsu.

“Lokacin da muka tambaye su dalilin da ya sa suka kashe su, sai suka ce dole ne mu ba su naira miliyan 10 da aka amince a kansu don su saki mahaifinmu da sauran mutane tara, in ba haka ba su ma za su gaya mana inda za mu je mu dauki gawarwakinsu.

“Ba mu iya daukar gawarwakin ba saboda sun riga sun rube. Dole muka binne su a can, ” inji shi.

Ya ce mahaifin nasu, wanda ke da mata uku da ’ya’ya 17, ya kusan shekara 78 kuma ba su da wani abin da za su ba masu garkuwar bayan naira miliyan 5, wanda aka tattara a tsakaninsu kuma tuni aka mika masu.

Ya kara da cewa ba su san ofishin tsaro da ya dace su tuntuba kan wannan batun ba saboda an sace su a Kastina kuma sun samu gawarwakin mutanen hudu a garin Kuyallo, Jihar Kaduna.

“Ba mu taba tunanin za mu tsinci kanmu a cikin irin wannan halin ba. Muna dai jin irin wannan labarin a wasu wurare amma hakan ya faru da mu. A yanzu haka dukkanmu mun gaji kuma ba mu san abin da za mu yi don tara sauran naira miliyan 5 don ceto mahaifinmu da sauran mutane ba.

“Muna kira ga gwamnati da mutane da cewa don Allah su taimaka su kubutar da mu. Ba mu da komai kuma ba mu da kowa. Don Allah muna bukatar taimakonku,” ya yi roko cikin hawaye.

A kan Mauludin da ya kamata mutanen su halarta, dan malamin ya ce an dage taron saboda mahaifinsu shi ne shugaba kuma ya kasance bako mai jawabi a taron tsawon shekaru.

KU KARANTA KUMA: Barayi sun afka gidan jarumin Kannywood, sun yi awon gaba da sabuwar motarsa da wasu muhimman kayayyaki

Ya kara da cewa wadanda suka shirya Mauludin sun yi alkawarin zuwa Kano kan batun amma har yanzu ba su zo ba.

A wani labarin, 'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon Ministan Wasanni, Damishi Sango, da ke jihar Filato.

Jaridar The Nation ta samu labarin sun kai hari gidan nasa da ke Danwal, Ganawuri bayan Vom, a karamar hukumar Riyom da misalin karfe 9:00 na daren Laraba.

A cewar rahotanni, an harbe wasu jami'an tsaro biyu da wani yaro yayin harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel