Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da jami’in tattara sakamakon zabe a Abia

Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da jami’in tattara sakamakon zabe a Abia

- Wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da jami'in tattara sakamakon zaben na jam’iyyar APC a zaben maye gurbi a Abia

- An sace Ozomena, wanda kuma shi ne Jami’in Kamfen na Mascot Uzor Kalu, dan takarar Jam’iyyar APC a yankin da sanyin safiyar ranar Asabar

- Sai dai kakakin rundunar 'yan sandar jihar, SP Geoffrey Ogbonna, ya ce ba shi da masaniya game da satar

An yi awon gaba da daya daga cikin jami’an tattara sakamakon zaben na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben maye gurbi na mazabar tarayya ta Arewacin Aba da Aba ta Kudu.

Wanda abun ya ritsa da shi mai suna Injiniya Mike Ozoemena shine jami'in tattara kuri'u na jam'iyyar APC a karamar hukumar Aba ta arewa a jihar Abia.

An tattaro cewa yan bindiga sun sace Ozomena, wanda kuma shi ne Jami’in Kamfen na Mascot Uzor Kalu, dan takarar Jam’iyyar APC a yankin da sanyin safiyar Asabar.

Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da jami’in tattara sakamakon zabe a Abia
Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da jami’in tattara sakamakon zabe a Abia Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Babu dan siyasa na hakika da zai yi watsi da damar zama shugaban kasa – Fayemi

A cikin zantawarsa da jaridar Daily Trust ta wayar tarho, Kakakin Jam’iyyar APC a Abia, ya ce kokarin da aka yi don gano inda Ozomena yake ya ci tura.

“Wasu maza sun yi awon gaba da Injiniya Mike Ozoemena, Daraktan Yada Labarai na Kamfen din Mascot Uzor-Kalu kuma jami'in tattara kuri'un APC a Aba ta Arewa a cikin farin Hilux daga shiyyarsa zuwa wani wuri da ba a sani ba.

“Ba mu san inda yake ba. Ba mu san inda suka kai shi ba; muna kira da a gaggauta ceto shi,” in ji shi.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandar jihar, SP Geoffrey Ogbonna, ya ce ba shi da masaniya game da satar domin har yanzu jam'iyyar ba ta kai kara ofishin' yan sanda ba.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsayar da zaben ranar Asabar bayan an ayyana kujerar Ossy Prestige, dan majalisar da ke wakiltar mazabar a matsayin babu kowa.

KU KARANTA KUMA: Madalla: 'Yar Kano da dan Zamfara sun lashe musabakar Al-Kur'ani ta mata da maza

Prestige, wanda memba ne na All Progressive Grand Alliance (APGA) ya mutu a asibitin Jamus a ranar 6 ga Fabrairu, 2021.

A wani labarin, ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, ya ce ba shi da wata alaka da baturen zaben da kotu ta jefa kurkuku kan taimakawa wajen magudin zabe.

Hakazalika Akpabio ya yi watsi da maganganun cewa baturen zaben ya taya shi da jami'yyar APC magudi a zaben.

Akpabio ya ce gaskiyan abinda ya faru shine shi aka yiwa magudi a zaben na 23 ga Febrairu, 2019.

Source: Legit.ng

Online view pixel