Yan bindiga: Idan zinare suke so, toh su nema mana sannan su bar mutanena su sarara, Sarkin Birnin Gwari

Yan bindiga: Idan zinare suke so, toh su nema mana sannan su bar mutanena su sarara, Sarkin Birnin Gwari

- Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, ya yi magana game da harin da aka kai wa ayarin motocinsa

- Basaraken ya bayyana cewa tsawon shekaru 20 kenan yan bindiga suna addabar yankinsa

- Ya ce idan har hakar gwal ne ke sa maharan damun yankinsa, toh su je su nema sannan su bar masa mutanensa su sarara

Mai martaba Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, ya yi magana game da harin da aka kai wa ayarin motocinsa.

Mai Gwari ya bayyana cewa idan 'yan fashi suna cikin yankinsa saboda gwal da suke da shi ne, toh a bari su neme shi sannan su bar mutane su sarara.

Da yake magana bayan harin, sarkin wanda ya ba da karin haske a kan harin ya ce gwamnan jihar ya gayyace shi zuwa wani taro a Kaduna.

Yan bindiga: Idan zinare suke su, toh su nema mana sannan su bar mutanena su sarara, Sarkin Birnin Gwari
Yan bindiga: Idan zinare suke su, toh su nema mana sannan su bar mutanena su sarara, Sarkin Birnin Gwari Hoto: BBC.com
Asali: UGC

"A karshe, na yanke shawarar neman sauki daga Sojojin Sama na Najeriya. Su ne suka kawo ni Kaduna a wannan yammacin. Haka Allah ya tsara.

KU KARANTA KUMA: Mun zabi yin garkuwa da mutane ne saboda shine hanya mafi sauki na samun kudi, yan bindiga

“Ba na cikin motar amma a bayyane ya ke cewa‘ yan fashin na harin motata ne, kuma Allah ya kiyaye direba na. Motata kawai aka lalata.

“Amma a fili manufar ita ce a kashe mu. Idan kun ga ramin harsasai a motata, a gilashin gaba da kuma gefen da nake yawan zama, a bayyane take manufar shine a kashe mu, amma sai Allah Madaukakin Sarki ya nufi akasin haka.”

Da ya koma bangaren tarihi, babban basaraken na ajin farko ya bayyana yadda 'yan fashi suka mamaye yankin sa, jaridar Tribune ta ruwaito.

Ya ce 'yan fashin suna yankinsa tun 1994, cewa sun fara ne da satar shanu sannan daga baya suka koma ga fashi da makami sannan kuma a yanzu suna satar mutane.

“Ta kai, a duk lokacin da mutanenmu ke tafiya, za su ajiye wasu kudade a aljihunsu. Idan ka ki basu kudi, zasu buge ka.

“Daga baya sai suka ga hakan bai yi musu ba kuma sun gama satar shanun. Don haka suka koma ga satar mutane.”

Ya kara da bayyana cewa tsawon shekaru 20 da suka gabata babu wani aiki mai mahimmancin gaske a yankin saboda duk lokacin da suka yi niyan kawo wani aiki sai su ce babu zaman lafiya.

“Mutanenmu masu bin doka ne da son zaman lafiya. Amma wadannan yan fashin sun canza mana labarin mu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta tsare Shugaban PDP mai shekaru 80 a Oyo kan kisan kai

“Wasu suna cewa saboda tarin gwal din da muke da su ne, idan kuwa haka ne me yasa ba su nemi zinaren sannan su bar mutane su sarara ba?"

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya nuna goyon bayansa a kan amfani da karfi da kuma tattaunawa da 'yan fashin daji da ke kisa da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Ganduje ya jaddada cewa zama a tattauna da tubabbun 'yan fashi na da muhimmanci musamman ga mutanen da aka yi garkuwa 'yan uwansu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da sashin Hausa na BBC, a ranar Juma’a, 19 ga watan Maris.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel