Muna zuwa kanku, zamu zo kakkabo ku, Shugaban sojin sama ga 'yan bindiga

Muna zuwa kanku, zamu zo kakkabo ku, Shugaban sojin sama ga 'yan bindiga

- Shugaban sojin saman Najeriya yace suna shirin bi ta kan 'yan bindiga a fadin kasar nan

- Ya aike da jan kunnen ne yayin da ya kai ziyara sansanin sojin sama dake jihar Kaduna

- Ya ce suna dab da cika umarnin Buhari na ganin cewa sun kakkabe 'yan bindiga kafin damina

Isyaka Amao, shugaban dakarun sojin saman Najeriya yace rundunar sojin Najeriya ta shirya kakkabo 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane dake fadin kasar nan.

Shugaban yace sojojin sun kammala dukkan shirinsu na ganin bayan 'yan ta'addan da suka addabi kasar nan.

Jaridar The Cable ta ruwaito, ya sanar da hakan ne a ranar Laraba yayin wata ziyarar aiki da ya kai sansanin sojin saman Najeriya dake jihar Kaduna.

Shugaban sojin saman yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojin da su tabbatar da cewa jama'ar kasar nan sun koma gonakinsu kafin zuwan damina.

KU KARANTA: An kama tsohon dan gidan fursuna da aka yi wa rangwame yana siyar da miyagun makamai ga 'yan ta'adda

Muna zuwa kanku, zamu zo kakkabo ku, Shugaban sojin sama ga 'yan bindiga
Muna zuwa kanku, zamu zo kakkabo ku, Shugaban sojin sama ga 'yan bindiga. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon Garri, gyada, sikari da aka raba wurin kayataccen biki sun janyo cece-kuce

"Dakarunmu sun shirya tsaf wurin yakar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane," yace.

"Muna aiki tukuru wurin ganin cewa mun shirya aiki kuma muna kokarin hada kai da sojin kasa da sauran sojoji domin komai ya tafi lafiya.

"Sako na ga 'yan bindiga shine za mu zo kansu tare da sojin kasa, na ruwa da kuma sauran hukumomin tsaro domin kakkabesu a kasar nan."

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari da Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami sun ce kundin tsarin mulkin kasar nan ya baiwa shugaban kasa Buhari damar rike IGP Mohammed Adamu a kujerarsa iyakar son ransa.

Matsayarsu tana kunshe ne a wani martanin hadin guiwa da suka fitar sakamakon kalubalantarsu da Lauya Maxwell Opara yayi a kan karin wa'adin mulkin Adamu a lokacin da ya dace a ce yayi murabus.

A takardar da lauya Maimuna Shiru ta fitar a madadin Buhari da Malami, ta ce Adamu dan sanda ne mai aiki kuma zai iya mora daga karin wa'adin mulkinsa daga shugaban kasa Buhari.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel