'Yan bindiga sun far ma kasuwar Zamfara, sun kashe mutum daya tare da kona shaguna

'Yan bindiga sun far ma kasuwar Zamfara, sun kashe mutum daya tare da kona shaguna

- Yan bindiga sun kai farmaki wata kasuwa da ke garin Yar' Tasha a cikin unguwar Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara

- Maharan sun halaka mutum daya tare da jikkata wasu da dama a yayinda suka bude wuta a kan yan kasuwar

- Rundunar 'yan sandan jihar bata yi tsokaci ba kan lamarin a daidai lokacin kawo wannan rahoton

Wasu da ake zargin 'yan fashi da makami ne, sun kai mamaya wata kasuwa da ke garin Yar' Tasha a cikin unguwar Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, inda suka kashe a kalla mutum guda tare da jikkata wasu da dama.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a ranar Alhamis, 18 ga watan Maris.

Mazauna garin sun shaida wa jaridar cewa wasu mutane biyu kan babura dauke da muggan makamai sun zo daga bangarorin yamma da gabashin kasuwar inda suka bude wuta a kan 'yan kasuwar.

'Yan bindiga sun far ma kasuwar Zamfara, sun kashe mutum daya tare da kona shaguna
'Yan bindiga sun far ma kasuwar Zamfara, sun kashe mutum daya tare da kona shaguna Hoto: @PremiumTimesng
Source: UGC

Ana cin Kasuwar garin 'Yar Tasha a kowace ranar Alhamis inda ake cinikin dabbobi da kayan masarufi.

KU KARANTA KUMA: Ina son karin yara, Allah zai wadata ni - Yar arewa wacce ta haifi yara 17

Tana da nisan kilomita 25 arewa da garin Dansadau ko kuma kilomita 75 kudancin Gusau, babban birnin jihar, kuma ta sha ganin jerin munanan hare-hare a baya.

Wani mazaunin yankin, mai suna Alhaji Umaru 'Yar Tasha, ya ce masu laifin da ke dauke da muggan makamai sun yi wa kasuwar kawanya da misalin karfe 2:00 na dare sannan suka fara budewa yan kasuwar wadanda galibinsu ke harkar dabbobi da hatsi wuta.

"An jefa gaba daya kasuwar da garin da ke kusa da ita cikin rudani.

"Yan kasuwa suna ta gudu zuwa wurare daban-daban don tsira. Da yawa daga cikin yan kasuwar sun samu munanan raunuka.

"Na kasance a gaban gidana lokacin da na fara jin karar harbe-harbe, kuma cikin' yan sakanni, kowa ya gudu don tsira.

"Na kutsa kai cikin gidana na kulle kofa.

"A yanzu haka da nake magana da ku, ina cikin gidana kuma ina ganin hayaki ya turnuke daga rumfunan kasuwar da suka kone daga nan.

"Mafi yawa daga cikin 'yan kasuwar, wadanda a da suka yi watsi da kayansu, watakila ba za su dawo ba kuma wasu da suke da karfin hali sun dawo don kirga asarar da suka yi.

KU KARANTA KUMA: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana abun da yasa yan bindiga suka kai wa tawagarsa hari

"Da alama maharan sun janye. A yanzu haka, wani ya kira ya gaya min cewa gawar mutum ɗaya kawai aka gani.

"Amma maharan sun yi awon gaba da kayayyaki da dama, musamman dabbobi da kayan sawa."

Mazaunin ya kara da cewa "Gaskiya lokaci ne mai matukar muni a gare mu a nan."

Sai dai, ya ce agajin gaggawa da yan sandan da ke garin da ke kusa ya takaita lamarin.

Ya ce, maharan sun janye bayan da ‘yan sanda suka zo cikin motar yaki.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce zai amsa wa jaridar kuma bai yi hakan ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

A wani labari, rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit

Online view pixel