Yan bindiga sun sace mutane 4 a Abuja, sun nemi a biya N200m kudin fansa

Yan bindiga sun sace mutane 4 a Abuja, sun nemi a biya N200m kudin fansa

- An sake garkuwa da mutane a garin Kiyi da ke cikin Babban Birnin Tarayya

- Wasu mutane dauke da makamai sun afkawa garin a ranar Laraba sannan kuma suka sace akalla mutane hudu

- ‘Yan sanda sun ce suna nan kan bibiyar masu laifin da ke neman a biya su kudin fansa miliyan N200

Wasu ‘yan bindiga a ranar Laraba, 24 ga Maris, sun afka wa mazauna garin Kiyi da ke yankin Kuje na Babban Birnin Tarayya (FCT), inda suka sace a kalla mutane hudu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A cewar jaridar, wani Mista Salami Olalekan wanda ya kasance memba na ma'aikatan Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCTA) na cikin wadanda aka sace.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun cafke wani mai POS wanda ke taimakawa masu satar mutane wajen karbar kudin fansa

Yan bindiga sun sace mutane 4 a Abuja, sun nemi a biya N200m kudin fansa
Yan bindiga sun sace mutane 4 a Abuja, sun nemi a biya N200m kudin fansa Hoto: @republicjournal
Asali: Twitter

Legit.ng ta samu labarin cewa William Salami, wani babban yayan wanda aka sacen, ya ce masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 200, miliyan 50 kan kowane mutum.

Ya ce:

“Masu garkuwar sun kira mu a waya, suna bukatar N50m kan kowane mutum”.

An tattaro cewa ragowar mutane ukun da aka yi garkuwa da su hadar da wani direban tasi, dan acaba da kuma wani daban.

An kuma ruwaito cewa ’yan bindigar sun shiga gidan daya daga cikin mutanen ta taga, tare da yin awon gaba da shi zuwa cikin daji.

Kakakin ’yan sandan birnin tarayya, Abuja, ASP Miriam Yusuf, ta tabbatar da sace mutanen, inda ta ce Rundunar na kokarin ceto su.

KU KARANTA KUMA: Dan Allah ka farka, kasar nan na wargajewa - Baba Ahmed ga Buhari

A gefe guda, wasu yan bindiga sun farmaki yan sanda ya yin da suke sintiri a garin Ashaka, karamar hukumar Ndokwa ta gabas a jihar Delta.

Yan bindigan sun caka ma ɗaya daga cikin yan sandan wuƙa wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa kuma suka jikkata wasu sannan suka babbaka ma motar da yan sandan ke sintiri da ita wuta.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa maharan sun kori 'yan sandan da tsiya kuma suka yi gaba da makaman su.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng