Rikicin VAT: Babu abun da Arewa za ta rasa, in ji jigon APC

Rikicin VAT: Babu abun da Arewa za ta rasa, in ji jigon APC

  • Batun karbar harajin kaya na VAT na ci gaba da haifar da rashin jituwa tsakanin wasu gwamnonin jihohi da gwamnatin tarayya
  • Wasu gwamnoni karkashin jagorancin Gwamna Nyesom Wike sun ce jihar na da cikakken yancin karɓar harajin VAT daga mazauna cikinta da masu kasuwanci
  • A halin yanzu lamarin yana gaban kotu yayin da dukkan bangarorin da abin ya shafa ke jiran hukuncin da manyan kotuna za su zartar

Yayin da ake ci gaba da cece-kuce tsakanin wasu jihohi da gwamnatin tarayya kan wanda zai dunga karbar harajin VAT a Najeriya, wani tsohon ɗan majalisar wakilai ya ce babu abinda yankin arewa zai rasa.

Aminu Jaji, tsohon shugaban kwamitin majalisar wakilai kan tsaron cikin gida kuma jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce arewa za ta ci gaba da harkoki idan kudu ta dage kan karbar VAT.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi alkawari Gwamnatinsa za ta kammala ayyukan da ta fara kafin ya bar mulki

Rikicin VAT: Babu abun da Arewa za ta rasa, in ji jigon APC
Rikicin VAT: Babu abun da Arewa za ta rasa, in ji jigon APC Hoto: Hon. Aminu Sani Jaji
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Jaji ya ce yankin kudu ba zai iya tsorata yankin arewa kan rike harajin VAT da ake karba daga 'yan Najeriya da kasuwancinsu a jihohinsu mabanbanta.

Jaji ya ce damuwar arewa ta ta'allaka ne kan hadin kan Najeriya da wanzuwarta koda ba tare da rikicin VAT ba.

A cewar tsohon dan majalisar, jihohi a yankin arewa sun fara shirin kirkirar wasu hanyoyin samar da kudaden shiga baya ga VAT.

Ya ce:

"Lokacin da tsarinmu ya fara aiki, wadanda ke kokarin mallakar VAT za su firgita."
"Muna shiri a madadin arewa kuma idan ba saboda hadin kan kasar ba, a shirye muke dari bisa dari mu ce a basu VAT din."

VAT: Gwamnonin Arewa za su hada-kai da Gwamnatin Tarayya suyi shari’a da Jihohin Kudu

Kara karanta wannan

Likitoci sun yi sa'a ni ne a matsayin minista, Ministan Buhari ya koɗa kansa

A gefe guda, mun kawo cewa akwai alamu da ke nuna cewa gwamnatin tarayya da wasu gwamnonin jihohin Arewa za su kalubalanci hukuncin da kotu tayi a kan harajin VAT.

Babban lauyan gwamnati zai yi shari’a da gwamnatocin jihohin Legas, Ogun, Akwa Ibom da Oyo domin a warware gardama kan wanda zai rika karbar VAT.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin Ribas tana kalubalantar hukumar FIRS a kotun koli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel