Yanzu Yanzu: Na kai karar Malami gaban Buhari, kuma bai amince da dokar ta-baci ba a Anambra - Gwamna Obiano
- Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya bayyana cewa sam ba ra'ayin Shugaban kasa Muhammadu Buhari bane barazanar sanya dokar ta-baci a jihar
- Obiano ya kuma bayyana cewa ya yi karar Abubakar Malami, ministan shari'a a gaban Buhari kan haka
- Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da shugaban kasar a Abuja
Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya bayyana cewa barazanar sanya dokar ta-baci a jihar ba ra'ayin shugaban kasa Muhammadu Buhari bane.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Obiano ya bayyana hakan ne ga manema labarai na fadar Shugaban kasa bayan wata ganawa da Buhari a fadar villa, Abuja.
Ya ce ya kai karar Ministan Shari’a kuma Babban Atoni-Janar na Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami ga Shugaban kasa kan lamarin.
Dalilin da yasa na ki amincewa da bukatar gwamnoni na dakatar da takarar Obasanjo a karo na biyu, Atiku
Gwamnan ya kuma bayyana barazanar a matsayin abin takaici, yana mai mamakin dalilin da ya sa bai yi tunanin sanya dokar ta-baci a Jihohin Arewa ba a lokacin da 'yan bindiga ke ta kashe-kashe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Wannan magana ce mara dadi daga bakin Atoni-Janar na Kasar, Malami. Abin takaici ne sosai. Na kuma kai karar lamarin ga Shugaban kasa kuma wannan baya cikin littattafan Shugaban kasar saboda ya san Anambra ta kasance jihar da ta fi kowacce zaman lafiya a Najeriya tsawon shekaru bakwai da doriya.”
Ya ce zai kira Atoni-Janar na kasar ya bayyana masa zuciyarsa game da wannan shawara, inda ya jaddada cewa baya ga matsalar tsaro da ta gabata, Amambra ita ce Jiha mafi zaman lafiya a kudu maso gabas, kamar yadda jaridar Sun ta rahoto.
Babbar Magana: Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi barazanar kafa dokar ta baci a jihar Anambra
A baya mun kawo cewa, a ranar Laraban nan, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata iya kafa dokar ta baci a jihar Anambra idan akwai bukatar hakan, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
A cewar gwamnatin shugaba Buhari, zata ɗauki duk matakin da ya dace domin tabbatar da an gudanar da zaɓen 6 ga watan Nuwamba a jihar.
Antoni Janar, Abubakar Malami, shine ya faɗi haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labari jim kaɗan bayan taron FEC a fadar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng