Haduwar Instagram ce: Kyakkyawar budurwa ta bayyana yadda ta samu mijin aure

Haduwar Instagram ce: Kyakkyawar budurwa ta bayyana yadda ta samu mijin aure

  • Yanar gizo ta hada wasu matasa ‘yan Najeriya biyu sannan ta dasa soyayya a tasakaninsu har sai da suka yi aure a 2021
  • Chidera na duba wani maudu’in bikin aure ne lokacin da ta ci karo da shafin Chibueze sannan sai suka fara magana
  • Dangantakar ma'auratan ta tsira daga kananan maganganu sannan kuma ya mika bukatarsa na son aurenta

Kuna tsammanin kun san duk hanyar da intanet ke haɗa mutane? Labarin soyayyar Chidera da Chibueze na iya sa ku sake tunani.

Chidera tana duba maudu’in wani bikin aure wani lokaci a cikin shekarar 2019 lokacin da ta tsinci kanta a shafin Chibueze. Bikin da ya kirkiri maudu’in na abokinsa ne.

Haduwar Instagram ce: Kyakkyawar budurwa ta bayyana yadda ta samu mijin aure
Haduwar Instagram ce: Kyakkyawar budurwa ta bayyana yadda ta samu mijin aure Hoto: @bellanaijaonline
Source: Instagram

Bayan ta danna alamar ‘like’ a wasu hotunan da ke shafinsa, sai mutumin ya fara bibiyar shafinta. Matashiyar ta ce kyawunsa ya burgeta sannan kuma hakan ya jawo hankalin su zuwa ga junansu.

Read also

‘Yan Najeriya 4 da suka auri turawa da kyawawan hotunansu, 1 tana da 'ya'ya Mata 4 tare da mijinta

Ba da daɗewa ba wasu saƙo na al'ada suka biyo baya. Tattaunawar su ta haifar da kyakkyawar alaƙa a tsakanin su sannan kuma kibiyar soyayya ta harbe su.

Chidera ta ce a karon farko da ta ga Chbueze, yana da tsayi sosai. Matar ta ce duk da cewa alaka ta kullu tsakaninsu a shekarar 2018, kullen korona ya kawo shakuwa tsakaninsu.

Uwargidar ta ce mutumin ya nemi aurenta da zobe na musamman wanda ke da farkon haruffan sunayensu. Labarin soyayyarsu ya yi kyau kuma yanzu sun yi aure.

Kalli hotunan a kasa:

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin martanin a ƙasa:

kaytteemaurice ta ce:

"Abun da ke ciki a yanzu shine zuwa neman maudu'i ooo .... Ba zan dunga ɓata lokaci na a wannan Instagram din ba .... mazajen aure na nan ... sanin inda za a bincika shine batu."

Read also

Buhari ya yi alkawari Gwamnatinsa za ta kammala ayyukan da ta fara kafin ya bar mulki

chef_kohoko ta ce:

"Rigar daurin auren, fure mai gashi. Fulawa duk sun yi kyau sosai."

onyinyechukwu._ ta ce:

"Bari na je neman maudu'i na bikin aure."

An sha ‘yar dirama a wajen liyafar aure yayin da ango ya yi watsi da amaryarsa don rawa da wata budurwa

A gefe guda, wani ango ya ba mutane da yawa mamaki kan abun da yayi a filin rawa a wurin liyafar aurensa.

Angon da ba a bayyana ko wanene ba ya bar matarsa a inda suke zaune don yin rawa tare da wata budurwa da ta halarci bikin.

A cikin bidiyon da Lindaikeji Blog ta wallafa akan Instagram, abokan angon da sauran baƙin sun jinjina wa angon saboda matakin da ya ɗauka yayin da amarya ke kallo.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel