Dalilin da yasa aka tube kakana shekaru 100 da suka gabata - Sarkin Zazzau

Dalilin da yasa aka tube kakana shekaru 100 da suka gabata - Sarkin Zazzau

  • Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamali, ya bayyana dalilin da yasa aka sauke kakansa daga mulki shekaru 100 da suka gabata
  • A cewar Sarkin, an sauke kakan nasa ne sabida ya ki biyayya ga Turawan mulkin mallaka
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 7 ga watan oktoba, yayin bikin shekararsa ta farko a kan karagar mulki

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamali, a ranar Alhamis, ya ce an cire kakansa daga kan karagar mulki shekaru 100 da suka gabata ne saboda ya ki yin biyayya ga Turawan mulkin mallaka.

Da yake jawabi yayin bikin shekararsa ta farko a kan karagar mulki, sarkin ya ce ahlinsa sun shafe shekaru 100 suna jiran sarautar tun lokacin da aka cire kakansa, Sarkin Zazzau, Aliyu Dan Sidi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Dalilin da yasa aka tube kakana shekaru 100 da suka gabata - Sarkin Zazzau
Dalilin da yasa aka tube kakana shekaru 100 da suka gabata - Sarkin Zazzau Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jaridar ta nakalto shi yana cewa:

“An cire shi ne saboda ya ki yin biyayya ga Turawan mulkin mallaka, tare da wani kakan nawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wadanda suka ziyarci Lokoja sannan suka ga yanayin abubuwa sun zubar da hawaye sabida rashin adalcin da aka masu. Sarkin Gwandu, Muhammadu Aliyu; Sarkin Kano, Aliyu Na Sambo; Sarkin Zazzau, Kwasau, Sarkin Zazzau; Aliyu Dan Sidi; da Sarkin Katsina, Abubakar, duk sun kasance a Lokoja. Muna fatan samun irin wannan karamci nasu, kuma muna addu'ar Allah ya saka musu da aljanna."

Sarkin ya roki jama'a da su hada hannu wajen ciyar da masarautar gaba.

Tsohon sarkin Kano kuma Khalifa na Darikar Tijjaniya ta Najeriya, Muhammad Sanusi II, a cikin jawabinsa, ya bukaci sarkin da ya ci gaba da hakuri da hada kan gidajen da sauran dangi domin samun nasara a mulkinsa.

Kara karanta wannan

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Ya ce:

"Dukkan mu da Allah ya ba jagoranci ya kamata mu sani cewa kamar yadda annabi ya fada kan jagoranci, cewa shugabanci amana ce kuma a ranar Kiyama, dukkan mu za mu yi bayanin yadda muka yi amfani da wannan amana."

Matsalar tsaron da yankin Arewa ke fama da shi Abun damuwa ne matuka, Sarkin Zazzau

A gefe guda, Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara mamaye Arewa, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Sarkin ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su tallafawa gwamnatin tarayya a kokarin da take na kawo karshen matsalolin tsaro a faɗin ƙasa.

Bamalli, wanda ya nuna cancantar mahaifinsa ya zama sarki fiye da shi, ya yi kira ga masu hannu a matsalar tsaro da yan bindiga su tuba, domin kawo zaman Lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel