Wata sabuwa: Buhari na shirin tsige Atoni-Janar Malami da wasu ministoci 14

Wata sabuwa: Buhari na shirin tsige Atoni-Janar Malami da wasu ministoci 14

  • Wani rahoton kafar yada labarai ya nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala shirye-shirye don sallamar a kalla ministocinsa guda 15
  • A cewar wata majiya ta fadar shugaban kasa, daga cikin wadanda za a sallama har da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami
  • Sai dai kuma ta ce ya fara kamun kafa da wasu manyan na kusa da shugaban kasar don ganin ba'a sallame shi ba

Rahotanni sun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala shirye-shirye don sallamar a kalla ministocinsa guda 15.

Kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto, daga cikin wadanda za a sallama kafin karshen shekarar 2021 har da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

Wata sabuwa: Buhari na shirin tsige Atoni-Janar Malami da wasu ministoci 14
Wata sabuwa: Buhari na shirin tsige Atoni-Janar Malami da wasu ministoci 14 Hoto: Femi Adesina
Source: Facebook

Wata babbar majiya a gwamnati, ta shaidawa jaridar cewa Malami ta fara yunƙurin murƙushe shirye-shiryen.

Read also

Za ka iya karban bashi don aiwatar da Kasafin Kudin 2022, Shugaban Majalisa ga Buhari

Rahoton ya kuma nuna cewa Babban Jami'in Shari'an ya gana da manyan mambobin da ke kewaye da fadar Shugaban kasa domin su rinjayi Shugaban kasar don kada ya kore shi.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaida wa SaharaReporters cewa:

"Shugaba Buhari na shirin sallamar Ministoci 15 tare da Malami a saman jerin wadanda za a kora. Wani ya tsegunta masa kuma ya fara fafutuka sosai. Ba ya son a kore shi.
"Bugu da kari, yana samun goyan bayan dimbin 'yan siyasa masu cin hanci da rashawa, ciki har da manyan mambobin cabal saboda yana taimaka musu wajen lalata shari'ar cin hanci da rashawa.”

Buhari a ranar 1 ga watan Satumba ya kori Saleh Mamman, Ministan wutar lantarki; da Sabo Nanono, Ministan Noma da Raya Karkara.

Read also

Buhari ya yi alkawari Gwamnatinsa za ta kammala ayyukan da ta fara kafin ya bar mulki

Babban jigon APC a arewa ya gaya wa Buhari Minista na gaba da za a sauke daga aiki

A baya mun kawo cewa a tsaka da sauye-sauyen majalisar ministocin shugaba Buhari, an yi kira da a kori wasu ministocin masu ci wadanda ake zargin ba su aikin kwarai.

Daya daga cikin irin wannan ministoci da aka sako a gaba shine Ministan Tsaro, Bashir Magashi.

A jawabinsa a ranar Juma’a, 3 ga watan Satumba, Abdulmajid Danbilki Kwammanda, wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Kano, ya bayar da hujjar cewa bai taba samun kwarin gwiwa kan ikon Magashi na yin aiki a ma’aikatar ba tun bayan nadinsa.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel