Yanzu Yanzu: Gwamnonin kudu maso gabas sun yanke hukunci na ƙarshe kan shugabancin 2023

Yanzu Yanzu: Gwamnonin kudu maso gabas sun yanke hukunci na ƙarshe kan shugabancin 2023

  • Gabannin zaben 2023, gwamnonin kudu maso gabas sun ce ya kamata yankin su ya samar da shugaban kasar na gaba
  • Gwamna Umahi wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas ya ce yankin ya cancanci a yi masa adalci da daidaito
  • Gwamnan na jihar Ebonyi ya ce yankin da Igbo ke da rinjaye baya son duk wani ballewa

Abakaliki, jihar Ebonyi - Gwamnonin yankin kudu maso gabas sun roki dukkan jam'iyyun siyasar kasar da su zabi 'yan takarar shugaban kasa na 2023 daga shiyyar.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas kuma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, yayi wannan kiran ne a ranar Juma'a, 8 ga watan Oktoba.

Yanzu Yanzu: Gwamnonin kudu maso gabas sun yanke hukunci na ƙarshe kan shugabancin 2023
Gwamnonin kudu maso gabas sun yanke hukunci na ƙarshe kan shugabancin 2023 Ht: Mazi Nwonwu
Source: Facebook

Gwamna Umahi ya lura cewa yankin da Ibo ta mamaye ya sadaukar da abubuwa da yawa kuma dole ne a ba shi damar samar da shugaban kasar na gaba ko ta hanyar shiyya ko ta sabanin haka.

Read also

2023: Ina gabatar da Atiku ga 'yan Najeriya, babu dan takarar kudu da zai iya lashe zabe - Jigon PDP

Legit.ng ta tattaro cewa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron addu'o'i da gwamnatin jihar ta shirya a Cibiyar Ecumenical, Abakaliki.

Har wa yau, rahoton ya ce ya yi kira da a shigar da yankin a harkokin kasar, inda ya sake nanata cewa dole ne Najeriya ta yi wa yankin kudu maso gabas adalci da daidaito.

Gwamna Umahi ya ce yankin kudu maso gabas ba ya da sha’awar Biyafara amma yana son kasancewa cikin adalci da daidaiton Najeriya.

2023: Abin da ya sa ba za a iya amincewa da Inyamuri a zaben Shugaban kasa ba inji Jigon APC

A gefe guda, jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Legas, Joe Igbokwe yace ba za a yarda da ‘dan takarar shugaban kasa daga yankin Ibo a zabe mai zuwa na 2023 ba.

Read also

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

Punch ta rahoto Joe Igbokwe yana cewa mutanen kasar nan ba za su kada kuri’a ga Ibo, wanda zai yi amfani da kujerar shugaban kasar wajen raba Najeriya ba.

Igbokwe wanda yana cikin masu ba Mai girma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, shawara ya bayyana wannan da ‘yan jarida suka yi hira da shi.

Source: Legit

Online view pixel