Yan bindiga sun kashe mutum 21 sakamakon bude wuta da suka yi a cikin kasuwa a Sokoto

Yan bindiga sun kashe mutum 21 sakamakon bude wuta da suka yi a cikin kasuwa a Sokoto

  • Akalla mutane 21 ne ’yan bindiga suka kashe bayan sun bude wuta a wata kasuwar da ke garin Unguwar Lalle a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto
  • Harin ya kuma jikkata wasu da dama, wadanda a yanzu suke samun kulawa a asibiti
  • An ce yan bindigar sun yi wa kasuwar kawanya ne sannan suka rika harbin kan mai uwa da wabi

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 21 ne suka rasa ransu a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin Sabon Birni da ke jihar Sokoto.

Kamar yadda sashin Hausa na BBC ya ruwaito, mazauna yankin sun ce maharan sun kaddamar da harin ne a lokacin da mutane ke cin kasuwar garin Unguwar lalle.

Yan bindiga sun kashe mutum 21 sakamakon bude wuta da suka yi a cikin kasuwa a Sokoto
Yan bindiga sun kashe mutum 21 sakamakon bude wuta da suka yi a cikin kasuwa a Sokoto Hoto: The Guardian
Source: UGC

An kuma tattaro cewa mutane da dama sun jikkata a harin, inda a yanzu haka suke kwance a asibitin garin Sabon Birni, yayin da wasu kuma aka tafi da su zuwa Sokoto.

Read also

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

A ruwayar Aminiya kuma, ta ce wani mazaunin yankin ya tabbatar mata cewa an kai hari ne a kan kasuwar wacce take ci sati-sati lokacin da ake tsaka da hada-hada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya nuna cewa zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa game da harin da kuma mutanen da aka kashe ba.

Sai dai kuma, tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni kuma hadimin gwamnan Sokoto shawara, Honarabul Abdullahi Mohammed Tsamaye ya tabbatar da afkuwar harin kasuwar na Unguwar Lalle.

Ya ce miyagun sun shiga cikin kasuwar sannan suka ta harbi ba kakkautawa inda suka kashe mutane tare da kone motoci.

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

A gefe guda, mun kawo a baya cewa wasu miyagu da ake zatton 'yan haramtaciyyar kungiyar sa-kai ne a jihar Sokoto, sun halaka mutane 11, ciki har da wani Limami, a kauyen Mamande da ke karamar hukumar Gwadabawa ta jihar.

Read also

'Yan bindiga sun kashe mutum 10, sun raunata wasu da dama a sabon harin da suka kai Katsina

Jaridar Daily trust ta rahoto cewa wadanda abin ya rutsa da su sun mutu nan take yayin da karamar hukumar ta kai wasu mutane hudu da samu raunin harbin bindiga zuwa asibiti domin yi musu magani.

Limamin wanda aka bayyana sunansa da Malam Aliyu an ce yana jagorantar Sallah a daya daga cikin Masallatan na yau da kullum a Salame.

Source: Legit

Online view pixel