Zangon karatu na 2021/2022: Jerin jami'o'in da suka sanar da ranakun zana jarabawar Post UTME

Zangon karatu na 2021/2022: Jerin jami'o'in da suka sanar da ranakun zana jarabawar Post UTME

Biyo bayan fitar da sakamakon jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire (UTME) na shekarar 2021, wasu jami’o’in Najeriya sun sanar da ranakun da za su yi Post-UTME.

Post-UTME ta kasance jarabawar sharar fagen shiga jami’a da dalibai kan rubuta domin tabbatar da ingancin sakamakon jarabawarsu ta UTME. Ita ke basu damar shiga manyan makarantun da suke so.

Zangon karatu na 2021/2022: Jerin jami'o'in da suka sanar da ranar zana jarabawar Post UTME
Zangon karatu na 2021/2022: Jerin jami'o'in da suka sanar da ranar zana jarabawar Post UTME Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Source: Getty Images

Legit.ng ta lissafo jerin jami'o'in da suka fitar da bayanai masu amfani dangane da Post-UTME a zuwa yanzu.

1. Jami'ar Legas (UNILAG)

UNILAG za ta yi gwajin Post-UTME daga ranar Litinin, 1 ga Nuwamba zuwa Juma'a, 5 ga Nuwamba 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar jami’ar, za a fara rajistan gwajin na Post-UTME na zangon 2021/2022 ta yanar gizo daga ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba zuwa Juma’a, 29 ga watan Oktoba, 2021.

Read also

Katsina: ‘Yan sanda sun kama tsohuwar ma’aikaciyar hukumar NIS bisa damfara ta N47m

Kudin tantancewar shine N2,000.

2. Jami'ar Nnamdi Azikwe

Jami'ar Nnamdi Azikwe ma ta fara siyar da fom na 2021/2022 Post UTME da na masu neman shiga aji biyu kai tsaye.

An fara atisayen a ranar Laraba, 8 ga watan Satumba kuma za a gama a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, 2021.

3. Jami'ar Jihar Delta, Abraka

Rijista ta yanar gizo ya fara a ranar Talata, 21 ga watan Satumba kuma za a rufe da karfe 6 na yammacin ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, 2021.

Jami'ar ta ce za a sanar da dalibai rana da kuma lokacin da za a tantance su a lokacin da ya dace.

An buƙaci dalibai da su ziyarci www.delsuonline.com don ƙirƙirar PIN (lamba) da kudi N2,000.

4. Jami'ar Ilimi ta Tai Solarin

A cewar BBC Pidgin, Jami'ar Ilimi ta Tai Solarin ta fara siyar da fom ɗin tantancewar Post UTME ta yanar gizo a ranar Litinin, 15 ga watan Satumba kuma za ta rufe a ranar Juma'a, 15 ga watan Oktoba.

Read also

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Za a gudanar da aikin tantancewar a babban harabar jami'a a ranar Laraba, Oktoba, 20.

5. Jami'ar Jihar Ribas

An fara rijistan shirin tantancewar Post UTME na jami’ar jihar Ribas a ranar Laraba, 8 ga watan Satumba kuma za a kammala a ranar Juma'a, 8 ga watan Oktoba.

Za a gudanar da aikin tantancewar daga ranar Litinin, 18 ga watan Oktoba, a cibiyar sadarwa da fasaha ta jami'ar.

6. Jami'ar Jihar Yobe

An fara rijistar kan layi don yin gwajin Post-UTME/DE don shigarwar 2021/2022 a ranar Juma'a, 1 ga Oktoba kuma zai ƙare ranar Lahadi, 31 ga Oktoba.

7. Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU)

An fara rajistar shirin tantancewa a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba kuma za a kammala a ranar Talata, 19 ga watan Oktoba.

Za a gudanar da aikin tantancewar ta yanar gizo.

Za a fara tantancewar Post UTME daga ranar Laraba, 27 ga Oktoba zuwa Juma'a, 29 ga watan Oktoba.

Read also

Da dumi-dumi: PDP na cikin matsala yayin da manyan 'yan majalisa 2 suka sauya sheka zuwa APC

Jerin jami'o'i 10 da aka fi daukan sabbin dalibai a Najeriya bana, Hukumar JAMB

A baya mun kawo cewa, rahoto da hukumar shirya jarabawar shiga jami'a a Najeriya (JAMB) ta saki ya nuna jami'o'i goma da aka fi daukan sabbin dalibai a 2020.

A labarin da Premium Times ta koro, wadannan jami'o'i goma suka dauki kashi daya bisa biyar na daliban Najeriya da suka shiga jami'a a shekarar 2020.

Legit ta tattaro cewa daga cikin dalibai 551,553 da suka samu gurbin karatu a jami'oin Najeriya kawo watan Agusta, jami'o'in nan 10 sun dauki dalibai 101,034.

Source: Legit.ng News

Online view pixel