Dalilin da yasa na ki amincewa da bukatar gwamnoni na dakatar da takarar Obasanjo a karo na biyu, Atiku
- Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya yi fatali da kiran da gwamnonin PDP suka yi na dakile takarar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a karo na biyu
- Atiku ya bayyana haka ne a taron kwamitin zartarwa na babbar jam'iyyar adawa ta kasa a Abuja a ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba
- A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, majalisar zartarwa ta PDP ta yanke shawarar cewa mulki ya ci gaba da kasancewa a kudu maso yamma na tsawon shekaru takwas
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na 2019, Atiku Abubakar ya bayyana dalilin da yasa bai goyi bayan kiran da gwamnonin jihohi suka yi ba don dakile takarar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na biyu.
Tsohon mataimakin shugaban kasar a ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba, ya ce ya ki amincewa da shawarar cewa ya yi takara da Obasanjo a inuwar jam’iyyar adawa a 2003, kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto.
Vanguard ta kara da cewa Atiku ya bayyana matsayinsa a yayin bude taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa a Abuja.
Maimakon amincewa da tsayawa takarar neman tikitin shugaban kasa na jam'iyyar a wancan lokacin, dan siyasar ya mika gwamnonin ga hukuncin kwamitin zartarwa na PDP na kasa
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwamitin sun yanke shawarar cewa mulki ya ci gaba da kasancewa a kudu maso yamma na tsawon shekaru takwas.
An nakalto yana cewa:
“Duk gwamnonin PDP da wasu mambobin jam’iyyar sun hadu da ni a Villa sannan suka ce ba za su goyi bayan Shugaba Olusegun Obasanjo a wa’adi na biyu ba, cewa ya kamata in tsaya takara.
“Sai na tura su ga hukuncin NEC inda NEC ta yanke shawarar cewa mulki ya ci gaba da kasancewa a kudu maso yamma na tsawon shekaru takwas.
“Ta yaya kuke so in saba wa hukuncin NEC sannan na ki amincewa, kuma muka ci gaba da harkoki. Don haka, kasar nan tana da yanayin adalci."
Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar
A gefe guda, jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar PDP a ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba ya amince da karkatar da matsayin shugaban jam’iyyar zuwa Arewa.
Hukuncin ya biyo bayan amincewa da shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton kwamitin karba-karba na babban taron jam’iyyar PDP na kasa wanda gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ke jagoranta.
Kwamitin karba-karba na Ugwuanyi ya musanya shugabanci da duk wasu mukamai na zababbun jam’iyyun da mutanen Arewa ke rike da su yanzu da na Kudu.
Asali: Legit.ng