Manyan Labarai A Yau
Shugaban jam'iyyar All Progressives congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sabon shaguɓe.
Kotun ƙasar Amurka ta yi fatali da ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya shigar a gabanata yana neman iznin duba takardun karatun Tinubu.
Dakaru sojoji sun aike da mayaƙan ƙungiyar ISWAP masu yawa zuwa inda ba a dawowa a wani gumurzu da suka fafata da su bayan sun daƙile harin da suka kai musu.
Reno Omokri ya yi magana kan buƙatar Najeriya ta sake dawo da doka da oda a Jamhuriyar saboda ƴan gudun hijira da baƙin haure da za su kwararo zuwa Najeriya.
Wasu ɓata gari da ake kyautata zaton ɓarayi ne sun janyo an tafka asarar sama da miliyan 70 a fitacciyar tsohuwar kasuwar Gombe bayan sun banka wa shaguna wuta.
Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin da ya sanka sauya sunan Dr. Maryam Shetty da na Mariya Mahmoud Bunkure cikin ministoci.
Gwamnatin sojoji a jamhuriyar Nijar ta yanke duk wata hulɗa da maƙociyarta Najeriya da wasu ƙasashe uku bayan zaman tattauna wa da neman maslaha ya ci tura.
Yayin da ake fargabar tashin yaƙi idan ECOWAS ta ɗauki matakin soji a kan jamhuriyar Nijar, an tattara jihohin Najeriya Bakwai da suka haɗa iyaka da Nijar.
Hambararren shugaban jamhuriyar Nijar, Muhammed Bazoum, ya roki ƙasar Amurka da sauran kasashen duniya karsu bari juyin mulkin da aka masa ya kai ga nasara.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari