Juyin Mulki: Reno Omokri Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Yakamata Najeriya Ta.Sake Dawo Da Daidaito a Nijar

Juyin Mulki: Reno Omokri Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Yakamata Najeriya Ta.Sake Dawo Da Daidaito a Nijar

  • Reno Omokri ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana buƙatar sake dawo da doka da oda a Jamhuriyar Nijar
  • Omokri ya ce yana da muhimmanci a sake dawo da doka da oda a Nijar saboda ƴan gudun hijiran da za su kwararo zuwa Najeriya
  • Ya ƙara da cewa Faransa, NATO ko Rasha ba su ba ne za su ji a jika ba kan rashin zaman lafiya a Nijar

Hadimin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya bayyana dalilin da ya sanya Najeriya yakamata ta sake dawo da doka da oda a Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.

Omokri ya bayyana cewa idan akwai halin rashin tabbas a Nijar, a bayyane yake masu gudun hijira za su yi ta kwararowa zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An Tsinci Gawar Hadimin Fitaccen Sanata Da Raunin Harsashi

Reno Omokri ya yi magana kan juyin mulkin Nijar
Reno Omokri ya nuna illar da rashin tabbas a Nijar za ta haifar wa Najeriya Reno Omokri/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter @renoomokri, ya bayyana cewa Najeriya na sa ido kan abubuwan dake faruwa a makwabciyarta, kamar yadda Rasha take sa ido kan abun da yake faruwa a Ukraine, haka Amurka ma take da Cuba.

Ƴan gudun hijira za su ƙwararo Najeriya idan babu zaman lafiya a Nijar

Ya kuma yi nuni da cewa kowane irin halin rashin tabbas da za a shiga a yankin Sahel, illar hakan kai tsaye ba za ta shafi Faransa, NATO ko Rasha ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Halin rashin tabbas a yankin Sahel ba zai zama illa kai tsaye ga Faransa, NATO ko Rasha ba. Libya da Chadi da su ke da iyaka da Nijar, suna cikin rikici. Aljeriya ba ta buɗe iyakokinta ga mutanen da ba Larabawa da waɗanda ba Amazigh ba. Mali tana cikin ƙalubale mai yawa da ya haɗa da ƙoƙarin karɓar mulki, ƴan tayar da ƙayar baya da yawan jama'ar da ya wuce ƙarfin tattalin arziƙinsu."

Kara karanta wannan

Buhari Ya Fadi Dalilin Ƙin Halartar Taron da Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban APC

"Saboda haka, idan akwai halin rashin tabbas a Nijar, a bayyane yake ƴan gudun hijira da baƙin haure cikin Najeriya za su kwararo."
"Hakan ya sanya ya zama wajibi kan Najeriya ta dawo da doka da oda a Nijar. Ko mu yi hakan ko mu kwaikwayi tsarin Trump na gina katanga a tsakanin mu da su."

ACF Ta Shawarci Tinubu Kan Amfani Da Soji a Nijar

A wani labarin kuma, ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta bayyana matakin da yakamata Tinubu da ECOWAS su ɗauka a Nijar.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa matakin tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulkin shi ne abinda ya fi dacewa ba wai amfani da ƙarfin soji ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel