Manyan Labarai A Yau
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da Farfesa Ngozi Okonjo-Iweala a fadar shugaban ƙasa tare da wani daga cikin ministocinsa da aka amince da shi.
Majalisar dattawa ta bayyana cewa akwai yiwuwar ƙila ta sake gayyatar Nasir El-Rufai da sauran ministoci biyu da ba a amince da su ba, don sake tantance su.
Sanata Solomon Adeola ya nuna godiyarsa bisa saƙonnin ta'aziyyar da ya samu kan rasuwar hadiminsa da ƴan bindiga suka halaka sannan ya sha alwashin gamo su.
AlmajiraI masu karatun Al-Qur’ani sun yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya janye sunan tsohon gwamnan jihar Kaduna daga cikin jerin sunayen ministocinsa.
Wata matar aure ta kadu yayin da ta isa wajen shagalin bikin mijinta sannan ta gano cewa aminiyarta ce amayar da yake yi. Ta hada yar dirama a wajen shagalin.
Wani Bakano mai suna Jaafar Lukman, yqa tsinci kansa a magarkama kan zargin raunata dan Jamila Mai-Kosai, wacce ta ki siyar masa da kokoda kosai a kan bashi.
Masu garkuwa da mutane sun sace basaraken garin Gurku da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, Jibril Mamman Waziri, da matarsa, Hajiya Sa’adatu Waziri.
Hargitsi ya ɓarke a majalisar dattawa a tsakanin sanatoci lokacin da majalisar ke tantance Festus Keyamo domin zama minista a gwamnatin Shugaba Bola Tinibu.
Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana dalilin da ya sanya Shugaba Tinubu bai naɗa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso muƙamin minista ba.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari