Kuma Dai: Malaman Musulunci Sun Nemi Tinubu Ya Cire Sunan El-Rufai Daga Jerin Ministoci

Kuma Dai: Malaman Musulunci Sun Nemi Tinubu Ya Cire Sunan El-Rufai Daga Jerin Ministoci

  • Wasu almajiran Sheikh Dahiru Bauchi sun bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya cire El-Rufai cikin ministocinsa
  • Sheikh Dahiru Bauchi, daraktan kula da harkokin ilimi a wata Gidauniyar Shehin malamin ya ce tsohon gwamnan Kadunan ya dandanawa almajirai kudarsu a lokacin da yake gwamna
  • Sun ce nada shi minista daidai yake da goyon bayan abun da ya yi masu a lokacin da yake da rigar kariya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gamayyar kungiyar masu karatu da haddar Al-Qur'ani sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin minista domin gaskiya, adalci, zaman lafiya da dorewar kasar.

Daraktan kula da harkokin ilimi a wata Gidauniya ta Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Bauchi a madadin malaman, Sheikh Sidi Aliyu Sise, ya bukaci Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan sannan kada ya rantsar da azzaluman yan siyasa.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Majalisa Ba Ta Tabbatar da El-Rufa'i Ba, Ta Amince da Mutum 45

Almajiran Dahiru Bauchi na so a cire El-Rufai cikin ministoci
Kuma Dai: Malaman Musulunci Sun Nemi Tinubu Ya Cire Sunan El-Rufai Daga Jerin Ministoci Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Dalilin da yasa muke so Tinubu ya cire El-Rufai a ministocinsa, malaman Musulunci

Ya ce zabar El-Rufai da tantance shi da majalisar dokokin tarayya ta yi rashin adalci ne ga masu karatu da masu haddar Al-Qur'ani, jaridar Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya dage cewa a cire sunan El-Rufai domin tabbatar da adalci, zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban kasa, rahoton The Sun.

Malamin ya ce:

"Yanzu wuka da nama na a hannun shugaban kasa, a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya, ya kamata ya duba kasar da idon basira, ya dubi halin da ake ciki, kada ya mika kai ga matsin lambar da ake yi wajen rantsar da El-Rufai mutumin da ya zalunci Almajirai a lokacin da yake matsayin gwamna.
"Muna neman a yi mana adalci sakamakon rashin adalci, cin zarafi, tashin hankali, da matsaloli da almajiranmu, malamanmu da malaman Alkur’ani da dama suka fuskanta, lokacin da ya kwashe almajiranmu da ba su ji ba ba su gani ba daga gidan Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ke Kaduna zuwa inda ba a sani ba.

Kara karanta wannan

Mariya Bunkure ta Bayyana a Majalisa, Ta Canji Maryam Shetty a Sahun Ministoci

"Muna son sanin laifinmu, wannan ne dalilin da yasa muke neman adalci daga gwamnatin tarayya saboda rantsar da El-Rufai a matsayin minista, za mu dauka cewa kana goyon bayan rashin adalcin da muka fuskanta a hannunsa ne a lokacin da yake gwamnan Kaduna.
"Yanzu da El-Rufai ya bar kujerar mulki, muna neman adalci maimakon gwamnati ta nada shi minista. Duk gwamnatin da ke alfahari da tafiya da adalci da gaskiya bai kamata ta ba mutane irin su tsohon gwamnan jihar Kaduna fifiko ba.
"Muna fatan shugaban kasa Tinubu zai fito fes kan lamarin El-Rufai, ta hanyar tabbatar da yi wa mutanen da ya zalunta a lokacin da yake matsayin gwamna adalci, a wancan lokacin yana sanye da rigar kariya kuma ba ma son zafafa tashin hankali don zaman lafiya duba ga yawan mabiyan Maulana Sheikh Dahiru Bauchi."

Cikakkun sunayen ministocin da majalisa ta tabbatar, jihohi da yankunansu

A baya Legit.ng ta kawo cewa majalisar dattawa ta tabbatar da wasu zababbun ministocin shugaban kasa Bola Tinubu bayan tantance su a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta.

Yayin zaman majalisar na ranar Litinin, Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa, ya sanar da tabbatar da mutane 45 cikin 48 da shugaban kasa Tinubu ya zaba, kamar yadda Legit.ng ta bibiyi shirin a NTA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel