Darajar Naira Ta Farfado Akan Dalar Amurka a Kasuwannin Canji

Darajar Naira Ta Farfado Akan Dalar Amurka a Kasuwannin Canji

  • Darajar Naira ta farfaɗo a farashin gwamnati da na ƴan kasuwa masu hada-hadar canji akan dalar Amurka
  • Hakan na zuwa ne bayan fargabar da masana da ƴan Najeriya suka nuna cewa darajar Naira ka iya komawa N1000/$1
  • Tun lokacin da CBN ya samar da farashin bai ɗaya na Naira, darajarta ta faɗi ƙasa warwas, inda aka yi fargabar abun zai yi muni sosai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Farashin Naira ya ƙaru akan dalar Amurka a kasuwannin I&E da P2P a ranar Juma'a, 11 ga watan Agustan 2023.

Wannan labarin mai daɗi na zuwa ne bayan farashin Naira ya yi faɗuwar da bai taɓa yi ba, inda ya kusa kai N1000/$1.

Darajar Naira ta farfado kan Dala
Darajar Naira ta farfado da kaso 5.2% Hoto: Benson Ibeabuchi
Asali: Getty Images

Farashin Naira na gwamnati

A kasuwar I&E, bayanai daga FMDQ sun nuna cewa an kulle kasuwar a ranar Juma'a farashin Naira yana a N740.60/$1.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Jerin Manyan Kasashe 10 Mafi Arhar Man Fetur a Nahiyar Afrika

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan na nufin darajar Naira ta farfaɗo da kaso 5.2 % ko N40.74 idan aka kwatanta da farashin N781.34/$1 da aka siyar da ita a ranar Alhamis.

Wannan tagomashin da Naira ta samu a ranar Juma'a ya faru ne bayan yawan hada-hadar kasuwar canjin ta ƙaru zuwa $164.60m daga $58.79m da aka samu a ranar Alhamis.

Farashin Naira a hannun ƴan kasuwa

A kasuwar P2P wacce ƴan 'crypto' ke amfani da ita, Legit.ng ta fahimci cewa darajar Naira ta farfaɗo zuwa N913/$1 a ranar Juma'a.

Wannan ci gaba ne idan aka kwatanta da farashin da aka siyar da ita na N940/$1 a ranar Alhamis.

Hakan yake a kasuwar ƴan canji inda aka siyar da Naira akan farashin N930/$1 saɓanin farashin N945/$ da aka siyar da ita a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Fetur Bai Gama Tashi ba, An Hango Yiwuwar Tashin Farashi Daga N615 Zuwa N750

Darajar Naira Ta Yi Mummunan Fadi

A wani labarin kuma, kun ji cewa darajar Naira ta yi mummunan faɗin da ba taɓa yi a tarihi, inda ta fadi ƙasa warwas akan dalar Amurka.

Darajar Nairar ta yi ƙasa ne bayan farashinta ya koma N950/$1 a kasuwar canjin kuɗi, inda aka samu ƙarin N50 a cikin kwana ɗaya kacal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel