Manyan Labarai A Yau
Tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, Gwamna Rotimi Akeredolu da sauran fitattaun yan Najeriya da aka yi karyan sun mutu a soshiyal midiya.
Kotun daukaka kara a kasar Angola ta tura wata yar TikTok mai suna Ana da Silva Miguel, gidan yari na tsawon shekaru biyu kan zagin shugaban kasarsu, João Lourenço.
Ƴan Najeriya sun yi martani kan musanta rage kuɗin buhun siminti da kamfanin Ɗangote. Da yawa ba su ji daɗin yadda farashin buhun siminti ya yi tsada ba.
Wata budurwa ƴar Najeriya ta yanke shawarar yanke alaƙar soyayyar da ke tsakaninta da wani matashi da ya nuna yana sonta, saboda kullum biredi ya ke ci.
Babban limamin cocin Revival and Restoration Global Mission, Fasto Kingsley Okwuwe, ya yi sabon hasashe game da shari’ar zabe da za a yi a kotun koli.
An hasko Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a wani bidiyo da ya yadu yana girkawa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki abinci.
Yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Israila da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu ya jawo asarar rayuka masu yawa. Ƴan ƙasashen waje da dama sun mutu, wasu sun ɓace.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhamadu Buhari, Hadi Sirika, ya samu sabon muƙami a gwamnatin jihar Katsina.
Farfesa Bolaji Akinyemi, tsohon ministan harkokin waje na Najeriya, ya bayyana cewa maƙasudin faɗan Isra'ila da Falasɗinu shi ne a kitsa yaƙin duniya na uku.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari