Manyan Labarai A Yau
Miyaguj ƴan ta'adda sun kai farmaki a jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da mnanoma masu tarin yawa suna tsaka da aikinsu na neman na abinci a gona.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shigar da sabbin shaidu na yin amfani da takardun bogi kan shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi martani kan rikicin da ake gwabzawa tsakanin Falasdinu da Isra'ila, ta buƙaci ɓangarorin biyu su hau teburin sulhu.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta musanta rahotanni da ke cewa ta yi watsi da daukaka karar da aka yi game da zaben gwamnan Kano na 2023.
Wani matashi dan Najeriya mai suna Prince Okebulu Ndukwo Nkobi, ya shirya tsaf don auren kyawawan yan mata biyu a rana daya. Za a daura auren a watan Nuwamba.
Miyagun ƴan bindiga sun kai hari a unguwar Dankali cikin ƙaramar hukumar Zaria a jihar Kaduna inda suka halaka mutum huɗu tare da sace wasu mutum biyar.
Kungiyar Hamas mai rajin kare Falasɗinawa, ta ƙaddamar da hare-hare a Isra'ila da sanyin safiyar ranar Asabar, 7 ga watan Oktoban 2023, a wasu birane.
Mataimakin shugaban jami'ar tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina ya bayyana dalilin da ya sanya ƴan bindiga suka sace ɗalibai biyar na jami'ar.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Abia, wanda ya tabbatar da nasarar Aƙex Otti.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari