Manyan Labarai A Yau
Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) ya sanar da waɗanda suka yi nasarar samun kwangilar bututun mai. Attajirai huɗu na Najeriya za su ƙara samun kuɗaɗe.
Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, ya sanar da tsige firaministansa tare da rusa majalisar ministocinsa, a ranar Juma’a, 6 ga watan Oktoba.
Kwamishinan yan sandan jihar Lagas, Idowu Owohunwa, ya bayyana abun da ake ciki a kan binciken marigayi mawakin Najeriya, Ilerioluwa Aloba, wanda aka sani da Mohbad.
Wani dattijo dan kasar Ghana ya tabbatar da cewar soyayya bata tsufa. A cikin wani bidiyo da ya yadu, an gano shi yana shawo kan budurwa domin ta amshi soyayyarsa.
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya gudanar da taron manema labarai kan takardun karatun shugaban kasa Bola Tinubu.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kebbi ta tabbatar da sahihancin zaɓen gwamnan jihar wanda gwamna Nasir Idris na jam'iyyar APC ya lashe.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya bayyana cewa kwamishinansa da ya shaƙi iskar ƴanci ba a biya ko sisi ba kafin a sako shi daga hannun miyagu.
Wata yar TikTok daga kasar Ghana, Sexydiva, wacce ke aiki a matsayin mai kula da dakin gawa ta bayyana cewa tana karbar albashi GH¢86,000 duk wata.
An samu tashin hankali a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba a majalisar dattawa bayan ministan Tinubu ya suma lokacin tantance shi sannan ɗan jarida ya rasu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari