Manyan Labarai A Yau
Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya taya shugaban kasa Bola Tinubu murna kan tabbatar da nasararsa da kotun koli ta yi a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.
A ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon shugaba da mambobin hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya (FCSC).
Kotun sauraron kararrakin zabe ta tsige dan majalisar jam’iyyar PDP, Destiny Enabulele, wanda ke wakiltar mazabar Ovia ta kudu maso yamma a jihar Edo.
Primate Ayodele ya yi hasashen abun da zai faru a siyasar jihar Ondo. A jihar, gwamna Rotimi Akeredolu ba shi da lafiya, kuma ana yunkurin tsige mataimakinsa.
Wata matashiyar budurwa ta saki bidiyon da ke nunawa mutane kazantaccen muhallin da take sarrafa man ja. Mutane da dama sun cika da mamaki bayan kallon bidiyon.
Ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar APC, Festus Keyamo, ya buƙaci Atiku Abubakar da Peter Obi su kira Shugaba Tinubu su taya shi murna.
Mai sharhi kan harkokin jama’a, Reno Omokri ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba.
Dakarun sojoji sun samu nasarar cafke wasu miyagun mutum biyu waɗanda ke safarar makamai ga ƴan ta'adda a jihar Kaduna. Sojojin sun kwato makamai.
Kotun koli za ta yanke hukunci kan karar da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP suka daukaka domin kalubalantar nasarar Shugaban kasa Bola Tinubu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari