Kai Tsaye: Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci a Karar Atiku, Obi Kan Nasarar Tinubu

Kai Tsaye: Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci a Karar Atiku, Obi Kan Nasarar Tinubu

A yau Alhamis, 26 ga watan Oktoba ne kotun koli za ta zartar da hukunci kan shari’ar su Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na jam'iyyar LP da ke kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, wacce ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu.

A wannan zauren, Legit Hausa za ta kawo maku karin bayanai daki-daki yayin da babbar kotun ke shirin zartar da hukunci kan makomar manyan yan siyasar Najeriya a yau.

Kotun koli za ta yanke hukunci a zaben shugaban kasa
Kai Tsaye: Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci a Karar Atiku, Obi Kan Nasarar Tinubu Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Kotun koli ta kori korafin Atiku kan Tinubu

A ci gaba da sauraran kararrakin zabe, kotun koli ta yi fatali da karar Atiku kan rashin hujjoji.

Kotun ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.Kotun ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.

Kotun koli ta ti raga-raga da manyan hujjojin Atiku da Obi

Kotun ta yi filla-filla da hujjojin da ‘yan takaran na jam’iyyun adawa su ka gabatar wajen kalubalantar nasarar Bola Tinubu.

Alkalan sun hadu a kan cewa babu inda doka ta wajabta samun 25% na kuri’un Abuja kafin dan takara ya yi nasarar lashe zabe.

Abin da sashe na 134 na doka ta ce shi ne mai neman takara ya tashi da akalla 25% a kaso biyu bisa uku na jihohin 36 da kuma Abuja.

Mai shari’a John Okoro ya rusa karar Chris Uche, SAN a madadin Atiku Abubakar na cewa ba a aika sakamakon zaben ta na’ura ba.

Kotun koli ta ce gazawar na’urar IREV ba ta nufin daina tattara sakamako.

Alkalan da su ka yi hukuncin sun ce rashin aikin IREV ba zai yi sanadiyyar da masu kada kuri’a za su samu wani rashin gamsuwa ba.

Kotun ta ƙi yarda da buƙatar Atiku ta shigar da sabbin hujjoji

A ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, kotun ƙoli ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar Atiku Abubakar wacce ba a waɗanda ba a tattauna kanta ba a kotun zaɓen shugaban ƙasa.

Kotun ta bayyana cewa tsarin doka bai ba kotun damar karɓar batutuwa waɗanda ba su fara biyowa ta babbar kotu ko kotun ɗaukaka ƙara ba.

Manyan batutuwa da Atiku da Obi suka gabatar a karar da suka daukaka a kotun koli

Atiku da Obi sun shigar da kara daban-daban domin kalubalantar hukuncin da kotun zaben ta yanke.

Ga wasu mahimman batutuwan da suka gabatar a cikin kararrakin:

  1. Cancantar takarar Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a zaben
  2. Rashin nasarar Tinubu wajen samun kaso 25 cikin 100 na kuri’un da aka kada a Abuja a lokacin zaben
  3. Gazawar INEC wajen tura sakamakon rumfar zabe zuwa shafinta a ainahin lokaci
  4. Zarge-zargen magudin zabe da aka yi don nasarar Shugaban kasa Tinubu
  5. Bayanan karatun Tinubu da Atiku ya samu daga jami’ar Jihar Chicago (CSU) a watan Oktoba

Kotun koli: An tsaurara matakan tsaro a harabar kotun gabannin yanke hukunci, bidiyo ya bayyana

Gabannin yanke hukuncin da kotun koli za ta yi a shari’ar da Atiku Abubakar da Peter Obi suka daukaka, jami’an tsaro sun mamaye harabar kotun.

An dauki wannan matakin ne da nufin dakile dul wani abu da ka iya kawo karan tsaye ga tsarin shari’ar.

Kalli bidiyon a kasa:

Yanzu Yanzu: CJN Ariwoola ya amince da watsa hukuncin kotun koli kai tsaye

Za a watsa hukuncin kotun koli kai tsaye a Talbijin.

Yan Najeriya za su iya bibiyar yadda zaman kotun ke gudana daga gidaje da wuraren aikinsu.

Shugaban Alkalan Najeriya, Kayode Ariwoola ne ya amince da wannan hukuncin.

Bidiyo ya bayyana yayin da jami’an DSS da yan sanda suka fara tantance harabar shiga kotun koli

Jami’an tsaro a harabar kotun koli sun fara tantance masu sa ido kan hukuncin karshe na yau.

An gano jami’an rundunar tsaro ta farin kaya (DSS) a cikin wani bidiyo da ya yadu suna jagorantar tawagar da ke gudanar da shirin tantancewar.

Online view pixel