Manyan Labarai A Yau
Akwai muhimman abubuwa da kotun ƙoli za ta yanke hukunci a kansu a ƙarar da jam'iyyun adawa da ƴan takararsu suka shigar kan ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda zai fara biyan limamai da masu unguwanni alawus-alawus domin su taimaka wajen magance matsalar tsaro a jihar.
Ƴan bindiga sun kawo harin ramuwar gayya a jihar Sokoto bayan sun rasa ɗaya daga cikin mutanensu. A yayin harin rayukan ƴan bindiga da dama sun salwanta.
Nyesom Wike zai karbe filaye a kan haraji a Abuja, Nyesom Wike wanda shi ne sabon Minista ya aika gargadin biyan haraji ga mutanen Abuja tun da ya shiga ofis.
Wani sabon rahoto da aka fitar ya fayyace gaskiya kan batun sakin shugaban shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Rahoton ya nuna cewa batun ba gaskiya ba ne.
Wani ɗan Najeriya ya koka inda ya caccaki bankinsa bayan ya gano cewa makuɗan kuɗaɗen da ya ciro a banki na jabu ne. Kuɗaɗen dai an ba shi su ne a Yuro.
Wani kwastoma ya fusata bayan ya rasa N500,000 a asusun ajiyarsa na banki, keastoman dai ya kinkimi man fetur inda ya yi yunƙurin cinnawa bankin wuta a Ogun.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a gidan wata babbar malamar jami'a ta jami'ar jihar Nasarawa tare da yin awon gaba da ita zuwa cikin daji.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun tare hanya a jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da mutane masu yawa. Cikin waɗanda ƴan bindigan suka sace har mai shayarwa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari