Kotun Koli: Babban Mai Adawa Da Buhari Ya Taya Tinubu Murna, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Atiku

Kotun Koli: Babban Mai Adawa Da Buhari Ya Taya Tinubu Murna, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Atiku

  • Shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu na ta samun sakonnin taya murna bayan kotun koli ta tabbatar da nasararsa a zabe
  • A ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba ne kotun koli ta sanar da Tinubu a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben 2023 tare da yin fatali da kararrakin da Atiku Abubakar ya shigar
  • Abun mamaki wasu gwamnonin PDP sun taya Shugaban kasa Tinubu murnar nasara da ya yi a kan Aiku da Peter Obi a koun koli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Benue - Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya shiga sahun masu taya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu murna kan tabbatar da nasarar zabensa da kotun koli ta yi.

Samuel Ortom ya taya Tinubu murnar nasara a kotun koli
Kotun Koli: Babban Mai Adawa Da Buhari Ya Taya Tinubu Murna, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Atiku Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Samuel Ortom, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Kotun koli: Ortom ya yi martani ga nasarar Tinubu, ya aika sako ga Atiku da yan Najeriya

Ya nanata cewa hukuncin kotun kolin babban nasara ce ga damokradiyya da yancin cin gashin kan cibiyoyin dimokaradiyyar kasar, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

“Dadina Da Gobe Saurin Zuwa”: Kalaman Mawaki Rarara Sun Tayar da Kura a Tsakanin Yan Najeriya

A cikin wata sanarwa da hadiminsa, Terber Akase ya saki a Makurdi, Orom ya roki yan Najeriya daga fadin jam'iyyun siyasa da su ajiye akidar siyasarsu sannan su marawa shugaban kasa Tinubu baya yayin da yake jan ragamar ci gaban kasar a wannan lokaci da kasar ke cikin wani hali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana da babban abokin hamayyar Tinubu, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan ya yi nuni kan cewa "yanzu lokaci ya yi da za a ajiye siyasa sannan a hada kai wajen marawa shugaban kasa baya a yayin da ya dauki babban nauyi na shugabanci", rahoton Punch.

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“Cif Ortom ya yaba ma jajaircewar shugaban kasa Tinubu wajen gyara tattalin arziki, wanda ka iya zama mai wahala a yanzu amma shakka babu zai haifar da sakamako mai kyau a gaba."

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Ganduje Ya Bayyana Shekarar da Ya Kamata Atiku da Peter Obi Su Yi Takarar Shugaban Kasa

Ortom ya shiga sahun jerin gwamnonin PDP da suka ziyarci Tinubu a baya-bayan nan don taya shi murna kan nasararsa a babban kotun.

Gwamna Adeleke na jihar Osun, Souye Diri na Bayelsa, da tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike sun ziyarci ofishin Tinubu tare da sauran jiga-jigan APC don taya shugaban kasar murna a ranar Alhamis, a fadar Villa da ke Abuja.

Jonathan ya ziyarci Shugaba Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya ziyarci Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan kotun koli ta yanke hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa a jiya Alhamis 26 ga watan Oktoba, Legit ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel