Manyan Labarai A Yau
An bayyana ɗan takarar da ke kan gaba a zaɓen gwamnan Kogi bayan bayyana sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 10 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ƙasa (INEC) ta yi.
Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta rubutawa Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) korafi cewa ta soke sakamakon zaben Kogi ta Tsakiya.
Dan takarar gwamnan jam'iyyar SDP a jihar Kogi, Murtala Ajaka ya lallasa Dino Melaye na PDP da Usman Ododo na APC wajen lashe kananan hukumomi biyar.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da kuɓutar da aka sace ana jajibirin zaɓen gwamnan jihar Bayelsa na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
Jam’iyyar PDP ta samu gagarumar nasararta ta farko a jihar Bayelsa a karamar hukumar Gwamna Duoye Diri yayin da INEC ta fara tattara sakamakon karshe.
Kotun ɗaukaka ƙara mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta tanadi hukunci kan ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau.
Gwamna Hope Uzodimma na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe kananan hukumomi 17 cikin 27 da aka sanar da sakamakonsu zuwa yanzu haka.
Wakilin jam'iyyar Labour Party (LP) a cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Imo, ya sha dukan tsiya ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen.
Dele Momodu hadimin Atiku Abubakar, ya caccaki hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) kan dakatar da zaɓe a wasu gundumomi tara a jihar Kogi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari