Farfesa Yakubu Yana Fuskantar Barazanar Zuwa Gidan Yari a Kujerar Shugaban INEC

Farfesa Yakubu Yana Fuskantar Barazanar Zuwa Gidan Yari a Kujerar Shugaban INEC

  • Ana zargin Farfesa Mahmoud Yakubu da sabawa hukuncin da kotun koli ta yi a kan shugabancin jam’iyyar APGA a Najeriya
  • Edozie Njoku ya tunawa shugaban INEC cewa Alkali ya bukaci Victor Oye ya daina ikirarin shi yake rike da jam’iyyar adawar
  • A cewar Njoku, shi babban kotun kasar nan ta ba gaskiya tun Mayu, kuma kin yarda da hakan zai kai mutum gidan gyaran hali

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC, Mahmoud Yakubu da jagoran jam’iyyar APGA, Victor Oye sun shiga cikin matsala.

Labarin da aka samu ranar Litinin daga This Day ya nuna za a iya daure Farfesa Mahmoud Yakubu da Victor Oye saboda saba umarnin kotu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da mukarrabansa sun daura haramar yin Umrah a ziyararsu ta Saudiyya

INEC.
Shugaban INEC, Mahmoud Yakubu da Bola Tinubu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Idan har wadannan mutane biyu su ka cigaba da yi wa kotu rashin biyayya kan hukuncin da aka zartar, za a iya daure su a gidan gyaran hali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban INEC zai je kurkuku?

Alkali ya bukaci a tabbatar da Cif Edozie Njoku a matsayin halataccen shugaban jam’iyyar APGA, amma hukumar ta INEC ba ta yi wannan ba.

Edozie Njoku ya bayyana cewa hukumar zabe ta na da kwanaki 14 ta yi biyayya ga hukuncin kotun da aka zartar tun ranar 9 ga watan Nuwamba.

Muddin ba ayi abin da kotu ta ce ba, an yi wa Alkali rashin da’a kuma an raina shari’a, hukuncin yin hakan shi ne zama a gidan gyaran hali.

Da aka yi hira da shi a karshen makon jiya a Abuja, ‘dan siyasar ya shaida cewa taurin-kan shugaban hukumar INEC zai iya jawo masa dauri.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da su ka taimaki APC, suka Kashe LP da PDP a zaben Gwamnan Imo

Laifin APGA da 'Yan NWC

Haka zalika rahoto ya ce Njoku ya ja-kunnen abokin fadansa a APGA watau Oye da duk sauran shugabannin jam’iyyar hamayyar na kasa.

Njoku ya tunawa majalisar gudanarwa ta APGA (NWC) cewa an kusa cinye wa’adin hukuncin Alkali Madugu ya yi tun watan Mayun bana.

Kotu ta tsige Oye - Njoku

A cewar Njoku, zaman da Oye yake cigaba da yi a matsayin shugaban APGA na kasa, ya ci karo da dokar kasa kuma an sabawa kotun koli.

Wanda ya shigar da karan ya ce kotu ta nuna dole ne duk wani wanda yake ikirarin shugabancin jam’iyyar adawar ya fice daga sakatariya.

INEC da zaben Jihar Kogi

Duk da Jam’iyyar APC mai-ci ta yi nasara a zaben sabon gwamna, ana da labari SDP da ADC sun kawo kananan hukumomi 8 da ke jihar Kogi.

Sanata Dino Melaye mai kuri’u 46,362 a zaben bana bai iya yin nasara ko da a kauyensa ba, Ahmed Usman Ododo ya samu nasara a Ijumu.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Hurowa Kotu Wuta Za a Canza Hukuncin Nasarar Sanatanmu - PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng