Miyagun Ƴan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 Tare da Sace Wani Babban Malamin Addini a Jihar Kwara

Miyagun Ƴan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 Tare da Sace Wani Babban Malamin Addini a Jihar Kwara

  • Ƴan bindiga sun salwantar da rayukan mutum biyu a wani hari da suka kai a ƙauyen Agbeku da ke ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara
  • Miyagun ƴan bindigan a yayin harin sun halaka matar wani babban faston cocin ECWA bayan sun dira a harabar cocin
  • Ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wani babban fasto na cocin ta ECWA da wasu mutum biyu a yayin harin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Wasu ƴan bindiga sun kashe mutum biyu ciki har da matar wani Faston cocin ECWA, Mrs Olawale a ƙauyen Agbeku da ke ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a daren ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, lokacin da ƴan bindigan suka dira harabar cocin da gidajen waɗanda lamarin ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun buɗe wa motar ɗalibai wuta, sun tafka mummunar ɓarna

Yan bindiga sun halaka mutane a Kwara
Miyagun yan bindiga sun kai sabon hari a Kwara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani shugaban al'ummar yankin, Rasaki Subair, a ranar ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, ya bayyana cewa ƴan bindigan sun yi awon gaba da Rabaran Oladunni, shugaban cocin ECWA ta gundumar Igbaja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Sun kashe Mrs Olawale, matar ɗaya daga cikin fastocin da ke da kantin sayar da kayayyaki, yayin da wani mutum kuma aka harbe shi yana can rai a hannun Allah a asibiti."
"Sun kuma ta fi da hadimar marigayiya Mrs Olawale da wani namiji ɗaya."

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Ƙoƙarin jin ta bakin kwamishinan ƴan sandan jihar a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, ya ci tura domin bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

Duk da cewa har yanzu rundunar ba ta naɗa mai magana da yawunta ba bayan ritayar Ajayi Okasanmi (SP), wani babban jami’in rundunar ƴan sandan ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun Buɗe wa mazauna garuruwa biyu wuta, sun kashe mutane da yawa

Jami'in ya ƙara da cewa:

"Muna ƙoƙarin samun cikakken bayani kan lamarin."

Ƴan Bindiga Sun Halaka Shugaban Jam'iyya

A wani labarin kuma, wasu ƴan bindiga da ba a tantance ko su waye ba, sun halaka shugaban jam'iyyar YPP na gundumar Nanka 1, Joe Mohel.

Ƴan bindiga sun halaka Mohel ne jim kadan bayan wata ganawa da mazauna yankin da mamba mai wakiltar mazabar Orumba ta Arewa da ta Kudu, Chinwe Nnabuife.

Asali: Legit.ng

Online view pixel