Manyan Labarai A Yau
An samu asarar rayukan mutum hudu a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da matafiya a kan titin hanyar Abuja-Kaduna. Wasu da dama sun jikkata.
Jam'iyyar All Progressives Congress, APC reshen jihar Kano, na zargin gwamnatin jihar ta NNPP da kokarin karkatar da kudaden kananan hukumomin jihar.
Rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da cafke wata daliba mai yin safarar bayanai ga yan bindiga a jihar. Dalibar ta yi bayanin alakarta da yan bindiga.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Kano, ta bankado shirin gwamnatin jihar na yin sama da fadi da Naira biliyan takwas daga asusun jihar.
Yan Najeriya sun yi martani mai zafi kan gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, bayan ya yi kiran da a yi wa gwamnatin Shugaba Tinubu addu'a ta samu nasara.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dau zafi kan harin da yan bindiga suka kai a kauyukan jihar Plateau. Shugaban kasar ya umarci jami'an tsaro su cafke miyagun.
Miyagun yan bindigan da suka sace basaraken kauyen Nkalagu Obukpa, sun sako shi bayan sun karbi makudan kudaden fansa da kayan abinci a hannun iyalansa.
Ministan jin kai da kawar da talauci, Dokta Betta Edu, ta fara biyan talakwa kdui N20,000 a Calabar, Cross River a kokarinta na kawar da talauci.
Wasu miyagun yan bindiga sun kai mummunan hari a wani ƙauyen jihar Sokoto, inda suka halaka mutum 12 tare da yin awon gaba da wasu mutane da dama.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari