Shehu Sani Ya Yi Ta'aziyyar Ghali Na'abba, Ya Bayyana Muhimmin Abu 1 da Ya Yi Domin Ceto Najeriya

Shehu Sani Ya Yi Ta'aziyyar Ghali Na'abba, Ya Bayyana Muhimmin Abu 1 da Ya Yi Domin Ceto Najeriya

  • Allah ya yi wa tsohon kakakin majalisar wakilai, Hon Ghali Umar Na'abba rasuwa a birnin tarayya Abuja
  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Saniɓya aike da saƙon ta'aziyyar marigayin wanda ya bayyana rasuwarsa matsayin babban rashi
  • Shehu Sani ya yi nuni da yadda a lokacin rasuwarsa, Ghali ya ceto dimokuraɗiyyar ƙasar nan lokacin da take cikin wani hali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya aike da saƙon ta'aziyya kan rasuwar Ghali Umar Na'abba.

Hon Ghali Umar Na'abba wanda tsohon kakakin majalisar wakilai ne, ya rasu a safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Disamba a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Labari da dumi-dumi: Tsohon shugaban Majalisa, Ghali Na’Abba ya bar duniya

Shehu Sani ya yi ta'aziyyar Ghali Na'abba
Shehu Sani ya yi ta'aziyyar rasuwar Ghali Na'abba Hoto: Shehu Sani, Abdulaziz Abdulaziz
Asali: Facebook

Tsohon sanatan a wani saƙon ta'aziyya da ya sanya a shafinsa na X (tsohon Twitter) ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya yi rayuwa mai inganci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yaba da jajircewarsa wajen ceto dimokuraɗiyyar ƙasar nan a daidai lokacin da ta tsinci kanta a cikin wani mawuyacin hali.

Shehu Sani ya yabi Ghali Na'abba

A cewar Shehu Sani da ba domin jajircewar irinsu Ghali ba, da tuni an cire wa'adin gwamnoni da shugabannin ƙasa daga cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

Ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya tsaya kan gaskiya da ƙwatar ƴanci, inda ya bayyana cewa rasuwarsa a matsayin babban rashi.

A kalamansa:

"Hon Ghali Umar Na'abba, tsohon kakakin majalisar wakilai. Ya yi rayuwa mai inganci. Ya ceci dimokuraɗiyyar Najeriya a daidai lokacin da take cikin wani hali."
"Ya kare tare da tsare martabar majalisa da ƴancinta. Ba tare da jajircewar irinsu Ghali ba, da an cire wa'adin mulkin gwamnoni da shugabannin ƙasa daga kundin tsarin mulkin mu. Ghali ya yi magana kan adalci kuma ya tsaya kan ƴanci. Babban rashi. Ina ta'aziyya ga iyalansa Allah ya ba shi Aljannar Firdausi. Amin."

Kara karanta wannan

Fitaccen Malamin Musulunci ya faɗi abinda zai faru da Bola Tinubu da tsohon Ministan Buhari a 2024

Gwamna Akeredolu Ya Rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akereredolu, ya yi bankwana da duniya.

Gwamnan wanda ya rasu a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, ya daɗe yana fama da jinyar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel