Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Harin Plateau, Ya Ba Jami'an Tsaro Sabon Umarni

Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Harin Plateau, Ya Ba Jami'an Tsaro Sabon Umarni

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da hare-haren ta'addanci da aka kai a ƙananan hukumomi biyu na jihar Plateau
  • Shugaban ƙasar ya yi umarnin da a gaggauta bayar da kayan agaji ga waɗanda suka tsira tare da ba da magunguna ga waɗanda suka jikkata a harin
  • Ya yi kuma umarni ga jami'an tsaro da su gaggauta zuwa yankin domin zaƙulo miyagun da suka aikata wannan ɗanyen aikin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Shugaba Bola Tinubu ya yi kakkausar suka kan munanan hare-haren da aka kai a ƙananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar Plateau, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama.

Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su gaggauta shiga cikin lungu da saƙo na yankin tare da kamo masu laifin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun kai ƙazamin hari ana shirin taron addini a arewa, sun kashe sama da 15

Shugaba Tinubu ya dau zafi kan harin Plateau
Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da hare-haren yan bindiga a Plateau Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ƙasa ya ba da umarnin ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 26 ga watan Disamba, ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kuma ba da umarnin a gaggauta tattara kayan agaji ga waɗanda suka tsira daga hare-haren na zalunci da kuma jinyar waɗanda suka jikkata.

Yayin da yake jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Plateau, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa mutanen da suka aikata wannan ɗanyen aikin ba za su tsira daga hukunci ba.

Ƴan bindiga sun halaka mutane a Plateau

Wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka mutum 16 a wani hari da suka kai a ƙauyen Mushu cikin ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Plateau

Ƴan bindigan sun.kai harin ne yayin da mutanen ƙauyen suke tsaka da barcinsu a ranar Asabar, 23 ga watan Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Shugaba Tinubu ya bayar da sabon umarni kan masu cin gajiyar N-Power

Ƴan Bindiga Sun Farmaki Ƙauyuka 23 a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa miyagun ƴan binɗiga sun kai mummunan hari a wasu ƙauyuka 23 na ƙananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi a jihar Plateau.

A yayin harin da ƴan bindigan suka kai, sun halaka mutum 145 tare da jikkata wasu mutane masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel