Manyan Labarai A Yau
Wasu miyagun yan bindiga sun ci karensu babu babbaka a wani sabon harin ta'addanci da suka kai a jihar Katsina. Miyagun yan bindigan sun halaka mutum tara.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya nada sabbin shugabanni a bankunan Polaris, Keystone da Union, biyo bayan korar tsofaffin shugabannin da bankin ya yi.
A kauyen Dele Jesus da ke jihar Gombe, an samu rahoton cewa wani matashi ya bankawa gidaje hudu wuta, inda suka kone kurmus. Hukumar NSCDC ta kama shi.
Bankunan Zenith da Jaiz sun fito sun yi magana kan rahotannin da ke yawo cewa hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta cafke shugabannin su.
Chidi Amadi, shugaban ma’aikatan Gwamna Sim Fubara, ya yi murabus. Kwamishinan labarai na jihar Ribas, Joseph Johnson, ya tabbatar da murabus din Amadi.
Sanata Shehu Sani ya caccaki Betta Edu kan jawabinta na baya inda ta ce gwamnatin Tinubu za ta fitar da yan Najeriya miliyan hamsin daga talauci.
Peter Obi ya bukaci Shugaban kasa Tinubu da ya kaddamar da bincike da kyau a ma’aikatar Betta Edu bayan badakalar kudi naira miliyan 585, yana so a hukunta saura.
Farfesa Pat Utomi ya ce ya tattauna da Peter Obi, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da sauran shugabannin adawa kan shirin kafa babbar jam’iyya a kasar.
Yan Najeriya sun yi martani yayin da ministan Abuja, Nyesom Wike ya ci karo da abokin karatunsa na sakandare yayin wani taron siyasa a jihar Ribas.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari