NSCDC Ta Kama Wani Matashi Saboda Bankawa Gidaje Wuta 4 a Gombe, Bayanai Sun Fito

NSCDC Ta Kama Wani Matashi Saboda Bankawa Gidaje Wuta 4 a Gombe, Bayanai Sun Fito

  • A kauyen Dele Jesus da ke jihar Gombe, an samu rahoton cewa wani matashi ya bankawa gidaje hudu wuta, inda suka kone kurmus
  • Hukumar tsaron farar hula NSCDC a jihar wacce ta samu nasarar cafke matashin ta ce lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba
  • NSCDC ta ce bincikenta na farko ya nuna cewa matashin ya samu sabani da wani dan uwansa, lamarin da ya fusata shi ya kona gidajen

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Gombe - Hukumar tsaron farar hula ta Najeriya (NSCDC) a jihar Gombe ta ce ta kama wani matashi da ake zargi da bankawa gidaje hudu wuta a wani kauye da ke jihar.

Kara karanta wannan

Aikin dan sanda: Dan Majalisa ya bankado yadda ake korar Hausawa yayin tantancewa a Jos

Kwamandan hukumar a jihar Mohammed Bello Mu’azu, ya ce lamarin ya faru ne da a daren ranar Laraba a unguwar Dele Jesus da ke karamar hukumar Balanga a jihar.

Matashi ya bankawa gidaje hudu wuta a Gombe
NSCDC ta kama wani mutum saboda bankawa gidaje wuta a Gombe. Hoto: @official_NSCDC
Asali: Twitter

Abin da ya sa matashin ya kona gidajen - NSCDC

Ya ce hukumar ta kama wanda ake zargin mai suna Segun Bulus dan shekara 27 biyo bayan samun bayanan sirri daga wasu jama'ar yankin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya kona gidaje hudu a cikin garin, lamarin da ya jawo barna mai yawa tare da rasa matsugunni ga masu gidajen.

The Punch ta tattaro cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne sakamakon wata hatsaniya da ta hada shi da kaninsa, amma dai hukumar na ci gaba da bincike.

Ba a sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja - Yan sanda

Kara karanta wannan

Badakalar $6bn: Kotu ta tura tsohon ministan Obasanjo gidan gyaran hali

A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta karyata rahotannin da ake yadawa na cewar an sace matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja a makon da ya gabata.

Rundunar reshen jihar Kaduna ta ce babu wanda aka sace, illa kawai dai jami'anta sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar, inda wasu matafiya shida suka samu raunuka.

A baya ne dai rahotanni suka nuna cewa 'yan bindiga sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja kuma har sun yi awo gaba da gomman mutane.

Wannan na zuwa ne bayan da hankulan jama'a musamman matafiya ya kwanta saboda saukin hare-haren 'yan bindiga da aka samu a hanyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel