Manyan Labarai A Yau
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kogi ta tabbatar da Ahmed Usman Ododo a matsayin zababben gwamnan jihar. Ta yi watsi da karar jam'iyyar SDP.
Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da cewa an samu rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar. Mutum biyar sun raunata.
Gwamnatin jihar Kano ta mika kokon bararta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Gwamnatin ta bukaci Tinubu ya shiga tsakani a rikicin masarautar Kano.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki wasu manufofin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar. Ya ce an tafka kuskure wajen aiwatar da su.
Gwamnatin jihar Kano ta hannun mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ta nemi afuwar Nuhu Ribadu kan zarginsa da hannu a rikicin masarautar Kano.
Rundunar sojojin Najeriya ta musanta cewa jami'anta na da hannu a rikicin masarautar Kano. Rundunar ta ce an tura sojojin ne domin hana karya doka da oda.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta gano shirin tayar da tarzoma a jihar da wasu bata gari ke yi. Ta yi gargadin cewa za ta cafke duk masu hannuna shirin.
Gwamnatin jihar Edo karkashin jagorancin Gwamna Godwin Obaseki ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma'aikata a jihar mai arzikin man fetur.
Wani masallaci ya rufto kan masallata a jihar Legas. Ana fargabar cewa mutane da dama ne da ke Sallah a cikin masallacin suka rasa rayukansu bayan aukuwar lamarin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari