Rikicin Masarauta: Bayan Ya Yi Barazana, Gwamnatin Kano Ta Ba Nuhu Ribadu Hakuri

Rikicin Masarauta: Bayan Ya Yi Barazana, Gwamnatin Kano Ta Ba Nuhu Ribadu Hakuri

  • Gwamnatin jihar Kano ta janye zargin da ta yi wa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na hannunsa a rikicin masarauta
  • Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda ya yi zargin ya nemi afuwar Malam Nuhu Ribadu
  • Aminu Abdulsalam ya bayyana cewa yaudarar gwamnatin aka yi kan bayanan da aka ba ta wanda hakan ya sanya ta zargi Ribadu da hannu wajen dawo da Aminu Ado Bayero zuwa Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta nemi afuwar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.

Gwamnatin jihar dai ta hannun mataimakin gwamnan jihar ta zargi Nuhu Ribadu da hannu a rikicin masarautar jihar.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

Gwamnatin Kano ta ba Nuhu Ribadu hakuri
Aminu Abdulsalam Gwarzo ya nemi afuwar Nuhu Ribadu Hoto: @Super_Joyce1, @NuhuRibadu, @Aminugwarzo
Asali: Twitter

Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zargi Nuhu Ribadu da taimakawa wajen dawo da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, zuwa Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Wace barazana Ribadu ya yi?

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron dai ya musanta hannu a lamarin inda ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan mataimakin gwamnan.

A cikin wata takarda, lauyoyin Ribadu sun bukaci neman afuwa daga mataimakin gwamnan jihar kan wadannan kalamai da ya yi na ɓatanci.

Gwamnatin Kano ta ba Nuhu Ribadu haƙuri

Sai dai Abdulsalam Gwarzo ya janye zarge-zargen nasa a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Mataimakin gwamnan ya kuma ba Nuhu Ribadu haƙuri, yana mai cewa an ba gwamnati bayanai ne marasa ƙamshin gaskiya, rahoton TVC ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Kano: Ribadu ya ɗauki zafi inda ya yi barazana ga Aminu Gwarzo, ya gindaya sharuda

"Mun ƙara yin bincike kuma mun gano cewa an yaudare mu sosai, kuma a madadin gwamnatin jihar muna so mu nemi afuwar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro."

- Aminu Abdulsalam Gwarzo

Batun rikicin masarautar Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta musanta cewa tana da hannu a rikicin da ke faruwa a masarautar Kano.

Kakakin rundunar Onyema Nwachukwu a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa jami'an rundunar da aka tura zuwa fada, an kai su ne domin hana karya doka da oda ba tabbatar da umarnin kotu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel