Manyan Labarai A Yau
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Wukari ta jihar Taraba. 'Yan bindigan a yayin harin da suka kai sun hallaka mutum biyu har lahira.
Hukumar kwastam ta yi alwashin kawo karshen masu boye kayan abinci a Najeriya domin kawo saukin kayan masarufi. Shugaban hukumar, Wale Adeniyi ne ya fadi haka.
Gwamnatin Tajikistan karkashin jagorancin Emomali Rahmon ta zartar da dokar da ta haramta mata sanya hijabi, da yara yin bukukuwan babbar Sallah.
Sarkin masarautar Akinale a jihar Ogun, Oba Olufemi Ogunleye ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a asibitin Landan ranar Laraba da yamma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani soja ya hallaka farar hula a birnin tarayya Abuja. Sojan ya yi wannan ta'asar ne bayan gardama ta barke tsakaninsu a kasuwa.
Jam'iyyar adawa ta Peoples Redemption Party (PRP) ta caccaki manufofin tattalin arzikim gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ta ce suna wahalar da 'yan Najeriya.
Wasu masu zanga-zanga sun dira gidan gwamnatin jihar Kaduna. Sun bukaci gwamnan jihar, Uba Sani, ya cafke magabacinsa Malam Nasir Ahmad El-Rufai.
Hukumar FIU ta kasar India ta lafta tara kan kamfanin hada-hadar kirifto na Binance kan zargin safarar kudade. Hukumar ta ci kamfanin tarar Dala miliyan 2.25.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya gayawa sababbin shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar cewa za su iya gudanar da ayyukansu daga ko'ina.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari