Manyan Labarai A Yau
Hukumar da ke yaki da masu yi wa kasa zagon kasa (EFCC) ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed a gaban kotu kan badakalar kudade.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta samu nasarar kwato N200bn a cikin shekara daya. EFCC ta sa an yankewa mutane 300 hukunci.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta musants rahotannin da ke yawo kan cewa ta nada mukaddashin hafsan sojin kasa. DHQ ta ce ko kadan ba ta yi wannan nadin ba.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya bukaci matasan Najeriya da su shigo a rika damawa da su a harkokin siyasa. Ya ce bai kamata su gujewa neman mulki ba.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun tare babban titin hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara. Tsagerun sun kashe muum biyu tare da yin garkuwa mutane masu yawa.
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya koka kan yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar nan. Ya ce nan gaba za su iya shiga Boko Haram.
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa ya taba yin cutar rashin ji ba tare da ya sani ba. Ya ce mutane da yawa na dauke da cutar.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar fatattakar 'yan bindiga a wani musayar wuta da suka yi. Sun ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Kashim Shettima ya wakilce shi a wajen taron CHOGM 2024 da za a yi. Za a gudanar da taron a ranakun 21 zuwa 26 ga Oktoba.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari