Badakalar N5.78bn: EFCC Ta Sake Gurfanar da Tsohon Gwamna a gaban Kotu
- Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kwara a gaban kotu
- EFCC ta shigar da sababbin tuhume-tuhume a kan Abdulfatah Ahmed da kwamishinansa na kuɗi kan zargin karkatar da N5.78bn
- An sake gurfanar da su a gaban kotu ne biyo bayan EFCC ta janye ƙarar da ta fara shigar da su a gaban babbar kotun jihar Kwara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kwara - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta sake shigar da wasu sababbin tuhume-tuhume 14 kan zargin almundahanar N5.78bn a kan tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfattah Ahmed.
EFCC ta shigar da tuhume-tuhume a kan Abdulfatah da kwamishinansa na kuɗi, Mista Ademola Banu, a gaban wata babbar kotun jihar Kwara ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Mahmud Abdulgafar.
Ana tuhumar mutanen biyu ne saboda zargin karkatar da kuɗin jama'a da aka ware da nufin gudanar da wasu ayyuka da kuma tsaron jihar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa EFCC ta sake gurfanar da mutanen?
Sake gurfanar da tsohon gwamnan da kwamishinan kuɗin ya biyo bayan janye ƙarar ne a makon jiya daga babbar kotun tarayya da ke Ilorin.
An janye ƙarar ne bayan an sauya alƙalin da ke sauraron shari'ar a babbar kotun tarayya da ke Ilorin, mai shari'a Evelyn Anyadike zuwa wata kotu.
Tun da farko EFCC ta fara gurfanar da Abdulfatah da Banu ne a kan tuhume-tuhume 12 na karkatar da kuɗin jama’a.
An je gaban mai shari’a Anyadike a ranar 29 ga Afrilu, 2024, inda suka ƙi amsa laifin da ake tuhumarsu da shi.
Sai dai kuma an sauya alkalin da ke jagorantar shari’ar wanda hakan ya sanya aka faro ta tun daga farko.
Hukumar EFCC ta ƙwato N200bn
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta kwato sama da N200bn a cikin shekara ɗaya.
EFCC ta kuma samu nasarar sanyawa kotuna su yankewa mutane kusan 3,000 hukunci a shekara ɗaya a ƙarƙashin jagorancin Ola Olukoyede.
Asali: Legit.ng