Manyan Labarai A Yau
Mutanen jihar Kaduna sun yi biris da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya domin zaben kananan hukumomin da ake gudanarwa a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya sake tarbar jagororin jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano zuwa APC bayan sun sauya sheka.
Wani jami'in dan sanda da ba a bayyana sunansa ba ya rasa ransa a jihar Legas. Dan sandan ya rasu ne bayan an kashe shi har lahira yana bakin aikinsa.
Ministan shari'a Lateef Fagbemi ya bukaci 'yan Najeriya da su daina korafi kan haƙin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar nan. Ya bukaci a kara hakuri.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya. Sojojin sun kuma kwato tarin makamai masu yawa.
Gwamnatin tarayya na yunkurin mayar da masu motoci amfani da iskar gas na CNG. Tsarin yana da saukin arha fiye da man fetur wanda ya yi tsada a Najeriya.
Majalisar dattawan Kenya ta kada kuri'ar tsige mataimakin shugaban kasar, Rigathi Gachagua kan cin hanci da rashawa da wasu tuhume tuhume 10 da ya musanta.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya caccaki bangaren shari'a kan abin da ya kira wasu hukunce-hukuncen da ba su dace a shari'o'in siyasa.
Kungiyar dattawan Arewa ta NEPG, ta yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kokarin da yake yi wajen magance matsalar rashin tsaron da ya addabi yankin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari